2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen

2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen

- Shugaban kungiyar kamfen din Next Level, Honourable Umar Waziri Kumo, ya bayyana cewa mutanen yankin arewa maso gabas za su marawa Buhari don ganin yayi nasara a 2019

- Ya ce hakan zai kasance ne saboda tarin ci gaba da gwamnatinsa ta kawo a mutanen yankin

- Kumo ya jadadda cewa harkar noma wanda shine babban aikin da mutanen yankin ke yi ya samu ci gaba sosai sakamakon jajircewar gwamnatin APC

Shugaban kungiyar kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari na Next Level, Honourable Umar Waziri Kumo, ya bayyana cewa mutanen yankin arewa maso gabas za su marawa Buhari baya kwansu da kwarkwatansu don ganin yayi nasara a zabe mai zuwa. Yace hakan zai kasance ne saboda tarin ci gaba da gwamnatinsa ta kawo a rayuwarsu.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 25 ga watan Disamba bayan wani ganawa da yan siyasa da matasan yankin wanda aka gudanar a Riveredge Hotel, Bauchi, Kumo, wanda hadimi ne na musamman ga shugaban kasar yayi ikirarin cewa gwamnatin tarayya tayi kokari sosai a yankin kama daga gina hanyoyi wanda ya hade dukkanin jihohin yankin shida da kuma yaki da ta’addanci inda yak are rayuka da dukiyoyin jama’a.

2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen
2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen
Asali: Depositphotos

A cewarsa, harkar noma wanda shine babban aikin da mutanen yankin ke yi ya samu ci gaba sosai sakamakon jajircewar gwamnatin APC.

KU KARANTA KUMA: Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa

“Wannan hujja ce an habbaka noman shinkafa da sauran kayayyakin abinci wanda yasa Najeriya ta zamo mai dogaro da kai wajen abinci."

Ya nuna yakinin cewa dan takarar shugaban kasa a APC zai kawo dukkanin yankin arewa maso gabas a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel