Yanzu Yanzu: APC ta ba Tinubu, Dangote da sauransu manyan mukamai (cikakken sunaye)

Yanzu Yanzu: APC ta ba Tinubu, Dangote da sauransu manyan mukamai (cikakken sunaye)

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ba babban jigon jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, da kuma babban attajirin dan kasuwan nan kuma biloniya Aliko Dangote mukamai a kungiyar kamfe din dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019.

Legit.ng ta tattaro cewa an saki cikakken sunayen mambobin kwamitin shugaban kasar a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba daga hannun babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina.

Tinubu wanda zai shugabanci kungiyar a gefe guda yayinda shugaban kasa zai yi jagoranci, na daga cikin kwamitin masu bayar da shawara na musamman ga shugaba Buhari. Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Dangote, Sanata Ahmed Lawan da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

Cikakken sunayensu:

Shugaba

President Muhammadu Buhari

Shugaba na biyu

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Mataimakan shugaba

1. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

2. Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole

Mataimakin shugaba a Arewa

SanataGeorge Akume

Mataimakin shugaba a Kudu

Sanata Ken Nnamani

Darakta Janar

Mai girma, Rt. Hon. Rotimi Amaechi

Mataimakin Darakta Janar (ayyuka)

Sanata A.O. Mamora

Mataimakin Darakta Janar (shiryawa)

Arch. Waziri Bulama

Sakatare

1. Adamu Adamu

2. Dele Alake

Daraktocin yankuna

a. Arewa maso yamma: Sanata Aliyu M. Wamakko

b. Arewa maso yamma: Sanata Muh’d Ali Ndume

c. Arewa maso tsakiya: Sanatar Abdullahi Adamu

d. Kudu mao yamma: Sola Oke, SAN

e. Kudu maso gabas: Sharon Ikeazor

f. Kudu maso kudu: Senator Godswill Akpabio

Daraktoci

a. Darakta, Kungiypoyin magoya bayan Buhari – Dr. Mahmoud Mohammed

b. Darakta manufofin sadarwa – Festus Keyamo, SAN

a. Mataimakiyar Darakta- Abike Dabiri- Erewa

c. Darakta, shiri – Hadiza Bala Usman

a. Mataimakin Darakta Kudu -Victor Eboigre

b. Mataimakin Darakta Arewa- Sanata Bashir Nalado

d. Darakta, tsare-tsaren zabe da kula– Babatunde Raji Fashola, SAN

a. Mataimakin Darakta I- Baba Kura Abba Jato

b. Mataimakin Darakta II- Chief Emani Ayiri

e. Daraktan dabaru – Dr. Pius Odubu

a. . Mataimakin Darakta - Senator Umanah Umanah

b. Mataimakin Darakta II- Nasiru Danu

f. Daraktan binciken manufofi- Farfesa Abdulrahman Oba

a. Mataimakin Darakta - Farfesa A.K. Usman

g. Daraktan matasa- Hon. Tony Nwoye assisted by the APC Youth Leader sadiq

a. Mataimakin Darakta Arewa- Barista Ismaeel Ahmed

b. Mataimakin Darakta Kudu– Jasper Azuatalam

h. Daraktan gudanarwa- Onari Brown

a. Mataimakin Darakta I- Chris Hassan

b. Mataimakin Darakta II- Abubakar Magaji Gasau

i. Daraktan mata- Jagorar mata Salamatu Baiwa

a. Mataimakin Darakta Arewa– Binta Mu’azu

b. Mataimakin Darakta Kudu– Adejoke Orelope Adefulire

j. Daraktan tsaro – Gen. A. Dambazzau

a. Mataimakan Daraktoci – Birgediya Janar Gambo da Mista U. Ukoma

k. Daraktan Doka – Emeka Ngige, SAN

a. Mataimakin Darakta - Farfesa Maman Lawan Yusufari

l. Daraktan ayyuka- Mallam Nuhu Ribadu

Manajan Daraktan kudi- Wale Edun

Mataimakin Darakta.Alhaji Adamu Fadan

Kwamitin masu ba shugaban kasa shawara na musamman

1. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

2. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

3. Sanata Ahmed Lawan (Shugaban majalisa)

4. Hon. Femi Gbajabiamila( Shugaban majalisar wakilai )

5. Shugaban APC na kasa Adams Oshiomole

6. Alhaji Aliko Dangote.

7. Mista Femi Otedola

Mambobin kungiya

1. Cif Bisi Akande

2. CifJohn Oyegun

3. Sanata Ita Enang

4. Dukka sanatocin APC masu ci

5. Dukkanin tsofaffin gwamnonin APC da masu ci

6. Mambobin APC a majalisar wakilai

7. Kwamitin masu ruwa da tsaki na APC

8. Dukkanin shugabannin mata na yankuna

Shugabannin jiha

1. Gwamnoni za su wakilci jihohinsu

2. Yan takarar gwamna a jihohin da ba APC ke mulki ba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel