Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu

Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu

- Buba Marwa ya bayyana cewa duk masu kokarin ganin sun mamaye fadar shugaban kasa ta Villa su jira har 2023

- Ya ce babu makawa shugaba Buhari zai dawo mulki a shekarar 2019

- Tsohon gwamnan na jihar Lagas a mulkin soja yace gwamnatin Buhari tayi kokari a fannin tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki

Tsohon gwamnan jihar Lagas a mulkin soja, Buba Marwa ya bayyana cewa duk masu kokarin ganin sun mamaye fadar shugaban kasa ta Villa su jira har 2023 domin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo mulki a shekarar 2019.

NAN ta ruwaito cewa Marwa ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, a garin Yola.

Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu
Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu
Asali: UGC

Marwa, wanda ya kasance shugaban kwamitin shugaban kasa akan miyagun kwayoyi yace yana da yakinin cewa shugaba Buhari zai kayar da sauran yan takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Ya ce: “Kungiyar Buba Marwa ce ta farko da ta shirya gangamin goyon bayan shugaba Buhari a 2016 saboda kkokarin da yayi a fanni uku na tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

“Idan Allah ya yarda zai dawo karo na biyu, don haka bani da shayin cewa duk masu son shiga Aso Villa su jira har 2023.”

Ta fannin tsaro yace hukumomin tsaro sun yi namijin kokari sannan kuma cewa suna bukatar goyon bayan al’umma baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel