Mahaifina ya dade baya magana – Babban dan marigayi Shehu Shagari

Mahaifina ya dade baya magana – Babban dan marigayi Shehu Shagari

- Babban dan marigayi Shehu Shagari ya bayar da bayani akan kwanakin karshe da mahaifinsa yayi a duniya

- Bala Shagari ya fada ma manema labarai a Sokoto cewa mahaifin nasa ya dade da daina Magana kafin mutuwarsa

Babban dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari ya bayar da bayani akan kwanakin karshe da mahaifinsa yayi a duniya.

Bala Shagari yace koda dai mahaifin nasa ya dade da daina Magana saboda halin rashin lafiya, ya dade yana da burin ganin an binne shi a gidansa da ke garin Shagari, jihar Sokoto a duk lokacin da Allah zai amshi ransa.

Mahaifina ya dade baya magana – Babban dan marigayi Shehu Shagari

Mahaifina ya dade baya magana – Babban dan marigayi Shehu Shagari
Source: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai a Sokoto a raar Lahadi, 30 ga watan Disamba Bala yace babu wani kalami na karshe da marigayi tsohon shugaban kasar ya furta saboda ya dade baya Magana saboda tabarbarewar lafiyarsa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa babban dan ya kuma yi bayani kan dalilin da yasa iyalan sun ki amsa tayin Sultan na Sokoto don binne mahaifinsu a makabartar Hubbare – inda ana ne aka binne gawar Shehu Usman Dan Fodio.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga

Ana ta sanya ran za a binne Shagari a wannan magabarta kasancewarsa Turakin Shagari, amma iyalan nasa sunce hakan shine burinsa wato a bisa shi a gidansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel