Zan hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai

Zan hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai

- Gwamnan El-Rufai na jihar Kaduna, ya sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa rikicin Kasuwar Magani

- Ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta zuba idanu kawai tana kallon masu laifin suna cin karensu ba babbaka ba

- El-Rufai ya ce duk wanda bincike ya bayyana yana da hannu a wannan rikici zai yaba ma aya zakinta

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta zuba idanu kawai tana kallon wadanda suka tada rikicin da ya auku a Kasuwar Magani ba.

El-Rufai ya ce duk wanda bincike ya bayyana yana da hannu a wannan rikici zai dandana kudan sa domin gwamnati za ta hukunta shi kamar yadda doka ya tanadar.

Zan hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai
Zan hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana haka ne a taron da yayi da mutanen garin Kasuwar Magani da kewaye inda ya shaida musu cewa lallai gwamnati za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a wannan rikici.

Idan ba a manta ba Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna, ya bayyana cewa an kashe mutane 55 a kazamin rikicin da aka yi a watan Oktoba, a garin Kasuwan Magani, cikin Karamar Hukumar Kajuru, a jihar Kaduna.

Kwamishina Ahmed Abdur-Rahman ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kaduna,sanna kuma ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 22 da ake zargi da hannu a wajen tayar da kayar bayan.

KU KARANTA KUMA: CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin hankali gabannin zaben 2019

Hakimin Kufana, Titus Dauda ya bada shawarar a karo jami’an tsaro a wannan yanki cewa hakanne kawai zai kawo karshen irin wannan tashin hankali da ake fama dashi a wannan yanki.

Suko kungiyoyin addinai na Musulmai da Kirista shawarar su daya ne cewa idan ba hukunta wadanda suke tada irin wannan tashin-tashina ake yi ba ba za a taba samun zaman lafiya ba. Sun kara da cewa gwamnati ta rika hukunta masu tada irin wannan rikici cikin gaggawa shine mafita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel