Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari

Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana karban rashawa zai fuskanci hukunci

- Ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da muryar Amurka

- Ya kuma yi kira ga shugabannin jiha da gwamnati da su bashi hadin kai wajen kama masu laifi ta hanyar satar kudin kasa ana yadasu a fadin duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana karban rashawa zai fuskanci hukunci.

“Duk wanda aka kama yana karban rashawa zai fuskanci doka,” inji shugaba Buhari a lokacin ganawarsa da muryar Amurka.

Shugaban kasar ya jadadda jajircewar gwamnatinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari

Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari
Source: Depositphotos

A cewarsa, an samu tarin nasarori zuwa yanzu akan yaki da rashawa ta hanyar bin ka’idoji da daidaito wajen yakin.

KU KARANTA KUMA: Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawo ba - Shehu Sani

Shugaba Buhari ya nanata bukatar ganin anyi nasara wajen yakar rashawa.

Ya kuma yi kira ga shugabannin jiha da gwamnati da su bashi hadin kai wajen kama masu laifi ta hanyar satar kudin kasa ana yadasu a fadin duniya.

Daga karshe Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga sabonta jajircewar gwamnati na hukumomin kasashen waje don ganin an cimma wannan manufa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel