Kalaman kiyayya: CAN ta gargadi El-Rufai akan hukunta Fasto Enenche

Kalaman kiyayya: CAN ta gargadi El-Rufai akan hukunta Fasto Enenche

- Kungiyar Kiristocin Najeriya ta gargadi Gwamna Nasir El-Rufai akan hukunta babban faston cocin Dunamis International Gospel Centre, Dr Paul Enenche

- CAN ta ce gargadin ya zama dole saboda rahotannin cewa za a gurfanar da Enenche kan kalaman batanci

- An yi zargin cewa furucin Enenche ya sake rura wutan kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi a Kasuwan Magani a da na Agom Adara, Dr Maiwada Galadima

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta gargadi Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna akan hukunta shugaba kuma babban faston cocin Dunamis International Gospel Centre, Dr Paul Enenche.

CAN a wani jawabi daga kakakin ta, Fasto Bayo Oladeji a ranar Laraba, 26 ga watan Disamba ta ce gargadin ya zama dole saboda rahotannin cewa za a gurfanar da Enenche kan kalaman batanci.

An yi zargin cewa furucin Enenche ya sake rura wutan kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi a Kasuwan Magani a ranar 18 ga watan Otoban 2018, da kuma kashe Agom Adara, Dr Maiwada Galadima da aka yi a ranar 26 ga watan Oktoba, 2018.

Kalaman kiyayya: CAN ta gargadi El-Rufai akan hukunta Fasto Enenche

Kalaman kiyayya: CAN ta gargadi El-Rufai akan hukunta Fasto Enenche
Source: Depositphotos

Don haka, kungiyar CAN ta ce yayinda take kyamar kalaman kiyayya, akwai bukatar a kawo tsari da zai tantance kalaman kiyayya.

Kungiyar ta ce hujja kawai Enenche ya kafa akan wani labari kan yadda aka kashe wani sarki na Kirista.

KU KARANTA KUMA: An kama yan sanda 4 da lafin fashi a Lagas

CAN ta ce El-Rufai ba zai iya daukar zafi da yawa akan haka ba domin shi kansa ya sha yinkaaman kiyayya a baya.

Kungiyar ta yi mamakin dalilin da yasa gwamnan ya gaza gurfanar da wadanda suka yi kisan ba maimakon son gurfanar da wani malami akan fakewa da kalaman kiyayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel