Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

- Kungiyar makiyayan Miyetti Allah ta bayar da tabbacin kawo wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u miliyan 20 a zaben 2019

- Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Kirowa, yayi wannan alkawarin a wajen taron kungiyar na shekara-shekara wanda aka gudaar a Abuja

- Kungiyar ta yaba ma kokari da ci gaban da gwamnatin Buhari ta kawo a fadin kasar

Kungiyar makiyayan Najeriya na Miyetti Allah ta bayar da tabbacin kawo wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u miliyan 20 yayinda kasar ke shirye-shirye akan zaben 2019.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Kirowa, yayi wannan alkawarin a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba wajen taron kungiyar na shekara-shekara wanda aka gudaar a Abuja.

Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah
Source: UGC

“Muna wakiltan mutane sama da miliyan 20 a fadin kasar, anan wajen muna da mutane 2,000 da suka zo daga sassa daban-daban na kasar.

“Muna da wakilai daga kowace karamar hukuma, kuma kun ji ra’ayinsu, sun kaddamar da ra’ayinsu akan Muhammadu Buhari domin ya kai su mataki na gaba.

“Wannan babban shawara ne na kungiyar. A matsainmu na shugabanni, bamu da zabi da ya wuce mu bi.

KU KARANTA KUMA: A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC

“MACBAN ta sha alwashin yin biyayya da marawa shugaba Buhari baya kan kokarinsa a kasar, ayyukan ci gaba da yayi da kuma sabonta tattalin arzikin al’umman kasar.

“Mun gode ma gwamnati kan shirin tallafi da ta bay an Najeriya ta hanyar ci gaban noma, musamman a fannin kiwo,” inji shi kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel