Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa

Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa

- Fadar shugaban kasar Najeriya ta saki wani gagarumin gargadi ga masu rike da mukaman siyasa, da jami’an gwamnati da jam’iyya

- Ta gargade su ne akan wofantar da mukamansu ta hanyar neman kudi da sunan Buhari

- Kakakin shugaban kasar yace za a dauki mataki akan masu aikata hakan

Fadar shugaban kasar Najeriya ta saki wani gagarumin gargadi ga masu rike da mukaman siyasa, da jami’an gwamnati da jam’iyya kan su daina aragizo don samun rara ta hanyar rashawa da kuma amfani da sunan shugaban kasa wajen neman kudi.

Hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu a ranar Talata, 25 ga watan Disamba a Abuja ya bayyana cewa yaudarar mutane da sunan fadar shugaban kasa na kawo tozarci ga fadar shugaban kasar.

Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa

Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa
Source: Depositphotos

A cewar Shehu: “Shugaban kasa Buhari ya rigada ya bayyana tun bayan rantsar das hi cewa ba zai yarda da kowani shashanci daga masu rike da mukamai, hadimai da jami’an gwamnati da ke banzatar da mukamansu don samun kudi ba bisa ka’ida ba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari sun kona gidaje kusa da garin Chibok

Hadimin shugaban yayi bayanin cewa amfani da mukamin gwamnati wajen samun alfarma rashawa ce, inda yayi gargadin cewa “Shugaban kasa ba zai aminta da kowani shashanci daga wani mutum bat a hanyar amfani da sunansa wajen damfarar mutane."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel