Jiragen ruwa 31 cike da kayayyakin amfani daban-daban za su isa tashar Lagas

Jiragen ruwa 31 cike da kayayyakin amfani daban-daban za su isa tashar Lagas

- Hukumar tashohin jiragen ruwa na Najeriya tace tana tsimayin jiragen ruwa 31 da zai kawo kayayyakin amfani daban-daban

- Ta ce hudu daga cikin jiragen za su taso da man fetur, sauran 27 kuma kuma za su dauko alkama, man jirgin sama, karafuna, kalanzir, da kuma kwantena

- Ta kuma ce jiragen ruwa 25 sun iso tashohin ruwa sannan suna jira a sauke alkama, kwantena, kalanzir da kuma man fetur

Hukumar tashohin jiragen ruwa na Najeriya tace tana tsimayin jiragen ruwa 31 da zai kawo kayayyakin man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani a tashar jirgin ruwa na Apapa da kuma Tin Can Island a tsakanin ranakun 27 ga watan Disamba 2019 da 12 ga watan Janairu, 2019.

Jiragen ruwa 31 cike da kayayyakin amfani daban-daban za su isa tashar Lagas

Jiragen ruwa 31 cike da kayayyakin amfani daban-daban za su isa tashar Lagas
Source: UGC

A cewar hukumar, hudu daga cikin jiragen za su taso da man fetur, sauran 27 kuma kuma za su dauko alkama, man jirgin sama, karafuna, kalanzir, da kuma kwantenan da ke dauke da kayayyaki daban-daban.

Ta kuma ce jiragen ruwa 25 sun iso tashohin ruwa sannan suna jira a sauke alkama, kwantena, kalanzir da kuma man fetur, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku

A wani lamari na daban, Mun ji cewa Najeriya ta kama hanyar zama daya daga cikin manyan kasashen da su ka fi kowa karfin tattalin arziki a Duniya, a cewar shugaban hukumar nan ta TETFund mai tallafawa manyan makarantu na kasa.

Dr. Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi ne shugaban hukumar TETFund na kasa, ya bayyana cewa alkaluma sun nuna lallai nan gaba za a rika kiran Najeriya a cikin kasashe 14 da su kayi fice ta fuskar tattalin arzikin kasa a Duniya baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel