2019: Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari

2019: Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari

- Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari

- Kungiyar da take tabbatar da hukuncinta tace kokarin Buhari a fadin kasar ya cacanci a yaba ta hanyar bashi damar kammala ayyukansa a zango na biyu

Kungiyar matasan Arewa, ta bayyana cewa ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019 domin ta yaba ma kokarin da yayi a kasar.

2019: Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari
2019: Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daraktan harkokin labarai na kungiyar ta kasa, Bello Abdulhamid ne ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a Kaduna.

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar da take tabbatar da hukuncinta tace kokarin Buhari a fadin kasar ya cacanci a yaba ta hanyar bashi damar kammala ayyukansa a zango na biyu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP yace Atiku na iya faduwa a zaben 2019

A wani lamari na daban, mun ji cewa Gwamna Akinwunmi Ambode yayi magana game da zaben 2019, inda yace irin dubban jama’an da ya gani wajen yakin neman zaben na APC ya tabbatar masa cewa shugaba Buhari ne zai sake lashe zaben da za ayi a farkon badi.

Gwamnan na Legas ya fadawa ‘yan jarida a Garin na Uyo cewa babu tababa lallai Buhari zai yi nasara a 2019. Ambode yace idan har dubban mutane za su fito wajen kamfen din Buhari, hakan na nuna cewa shugaban kasar zai zarce.

Kwanan nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman zaben sa a Garin Uyo da ke Jihar Akwa-Ibom. Jama’a da dama sun fito sun tarbi shgaban kasar a wani filin wasan kwallon kafa da ke babban birnin Uyo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel