Hadimin Tambuwal da wasu sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto

Hadimin Tambuwal da wasu sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto

- Mambobin jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP) 50,000, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Party (APC), a jihar Sokoto

- Cikin wadanda suka sauya shekar harda wani tsohon hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto

- Wamakko yayi maraba ga sabbin masu sauya shekar sannan ya basu tabbacin samun daidaito kamar kowani dan jam’iyya

Akalla mambobin jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP) 50,000, ciki harda wani tsohon hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Party (APC), a jihar Sokoto a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba.

Masu sauya shekar sun koma APC ne tare da tsohon shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Chika Umar Dantama, tsohon dan takarar dan majalisar dokokin jiha a jam’iyyar a 2015, da kuma jami’ai da dama.

Hadimin Tambuwal da wasu sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto
Hadimin Tambuwal da wasu sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto
Asali: Facebook

Da yake Magana a wajen taro, shugaban APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda ke wakiltan Sokoto ta arewa a majalisar dokokin tarayya, yayi maraba ga sabbin masu sauya shekar sannan ya basu tabbacin samun daidaito kamar kowani dan jam’iyya.

Wamakko ya ci gaba da cewa wasu manyan PDP sun dade da kowama APC, inda yayi bayanin cewa ba da dadewa ba za’a tarbe su zuwa jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu yarda a karawa IGP wa’adi a 2019 ba - Inji Kungiyar CUPP

Sanata Wamakko ya kuma isar da gaisuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga mutanen jihar Sokoto inda yace “kwanan nan zai ziyarci jihar, domin isar da gaisuwa ga mutanen jihar”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel