Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Jam’iyyar All Progressives Congress na kara yin karfi a jihar Gombe yayinda da zabe ke dada gabatowa. A yanzu haka wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar DPP, Nafiu Bala Gombe da yan PDP 250 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa ana zargin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Babayo Gamawa, wanda jam’iyyar ta dakatar, shi kuma ya koma APC, da rarumar kudade har naira miliyan 500.
Wannan kungiyar ta Yarbawa wato Afenifere, ta bayyana cewa hukuncin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya jagoranci tawagar kamfen dinsa, ba komai bace face yaudara.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya gabatar da adadin mutanen da aka yiwa rijistan zabe ga dukkan jam’iyun siyasa a zabe ai zuwa. Adadin masu zabe da aka yiwa rijista su 84,004,084.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, babu kasar da aka ci amanarta a duniya kamar kasar Najeriya, idan aka yi duba ga abinda shugabannin gwamnatocin da suka gabata suka yi tsawon shekaru goma sha shida.
Kungiyar fararen mayu a Najeriya ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kada ya maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a 2015, idan har yana son ya lashe zabe.
Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira bilyan 7.30 wajen hada-hadar shan mai da kula da jiragen zirga-zirgar Shugaba Buhari a shekarar 2019. Bayanan yadda za a kashe kudaden na kunshe a daftarin kasafin kudin wannan shekarar.
Rundunar sojin kasar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram sama da 280 a kusa da iyakar kudu maso gabas da Najeriya a kwanakin da aka yi ana kai mamaya ta kasa da sama, cewar ma’aikatar tsaro a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu.
Shekarar 2018 ta kasance cike da lamura daban-daban ga dandalin wasan Hausa na Kannywood kama daga mai dadi, ban al’ajabi, bakin ciki da dai sauransu. Hakan ya sa muka yi amfani da wannan damar wajen zakulo maku wasu daga ciki.
Aisha Musa
Samu kari