Buhari na amfani da kudaden gwamnati wajen yin kamfen – Atiku yayi zargi

Buhari na amfani da kudaden gwamnati wajen yin kamfen – Atiku yayi zargi

- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi shugaban kasa Buhari da jam’iyyar APCda saba dokar zabe na 2010, ta hanyar zargin amfani da kudaden jiha wajen kamfen din takarar shugaban kasa

- Atiku yace da Buhari da APC sun saba alkawarin da suka dauka na kin amfani da kudin jama’a

Tsohon mataimakin shugaban kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da saba dokar zabe na 2010, ta hanyar zargin amfani da kudaden jiha wajen kamfen din takarar shugaban kasa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku a wani jawabi da ya saki a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu ta hannun mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Paul Ibe, yace zargin yayi sabani da ikirarin shugaba Buhari da APC na cewa ba za su yi wasa da kudin kasar ba.\

Buhari na amfani da kudaden gwamnati wajen yin kamfen – Atiku yayi zargi

Buhari na amfani da kudaden gwamnati wajen yin kamfen – Atiku yayi zargi
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu, a watan Disamban 2018 ya gargadi masu rike da mukamai akan amfani da kudaden jama’a wajen yin kamfen.

Don haka Atiku, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari da APC na ta amfani da kudaden kasa ba bisa ka’ida ba wajen yiwa kansu kamfen din zabe.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji

A baya mun ji cewa Hajiya Titi Atiku Abubakar, uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ta roki yan Najeriya da su yi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, cewa gwamnatinsa ta rasa hanyarta.

Misis Abubakar ta yi wannan furucin neyayinda take jawabi a wani taro a Najeriya mai taken : ‘Kick Out Hunger, Kick Out APC’ wato ayi waje da yunwa, ayi waje da APC, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel