Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari

Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari

- Shugaban Buhari, ya bayyana cewa, babu kasar da aka ci amanarta a duniya kamar Najeriya

- Yace hakan na da nasaba da abinda shugabannin gwamnatocin da suka gabata suka yi tsawon shekaru goma sha shida

- Shugaban kasar ya bayyana cewa, gwamnatinsa bata iske komai ba a kasa a lokacin da ya hau karagar mulki a shekarar 2015

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, babu kasar da aka ci amanarta a duniya kamar Najeriya, idan aka yi duba ga abinda shugabannin gwamnatocin da suka gabata suka yi tsawon shekaru goma sha shida.

A hirar da muryar Amurka ta yi da shi, shugaba Buhari yace wanda yake gani sharri ne ko kuma bita da kulli gwamnatinsa ke yi wa gwamnatin da ta gabata, toh yaje turai yaga yadda ake cinikin mai da kuma kudaden da ake samu, daga nan ya bayyana inda kudin su ke.

Shugaban kasar ya bayyana cewa, gwamnatinsa bata iske komai ba a kasa a lokacin da ya hau karagar mulki a shekarar 2015.

Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari
Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari
Asali: Depositphotos

Dangane kuma da kasafin kudin da ya gabatar gaban majalisa, shugaba Buhari yace, kasafin kudin shekara ta dubu biyu da goma sha tara da gwamnatinsa ta gabatar ya maida hankali a kan batun hanyoyi, da tsaro, da biyan ma’aika da kuma samar da wutar lantarki.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu

A cewarsa, kasar China ta amince zata yi wadansu hanyoyin mota da hanyoyin jirgin kasa, da dam-dam na Mambila, karkashin yarjejeniyar da aka kulla na biyan kashi goma sha biyar bisa dari na kudin da ake bukata, yayinda Najeriya zata biya sauran bashin cikin shekaru ishirin da ruwa kadan, Yace idan aka gaza samun tonon mai kamar yadda aka zata sai a sake duba hanyoyin da za a bi domin cike gibin da aka samu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, yawanci basusukan da gwamnatinsa take biya ba ita ta ciwo su ba, ta gaje su ne daga gwamnatin da ta gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel