Yan iska sun kai hari yankin gidan iyalan Saraki, sun raunata mutum 11

Yan iska sun kai hari yankin gidan iyalan Saraki, sun raunata mutum 11

- Wasu yan iska sun kai mamaya yankin Agbaji da gidan iyala shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki yake

- Akalla mutane 11 aka raunata yayinda aka lalata ababen hawa 50 a harin

- Saraki ya bukaci mutanensa da su kwantar da hankulansu

Wasu yan iska sun kai mamaya yankin Agbaji da ke Ilorin, inda iyala shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ke a zama.

Akalla mutane 11 aka raunata lokacin da yan iskan suka kai mamaya yankin sannan suka lalata ababen hawa 50 a ranar Lahadi, 13 ga watan Janairu.

Haka zalika, an lalata masallatan Solagberu da Aligan, da kuma gine-gine biyar a yankin.

Lamarin a cewar mazauna yankin ya fara da misalin karfe 11:30 na safe lokacin da wasu yan iska dauke da makamai suka iso yankin sannan suka fara harbi a saba don su tsorata mutane.

Yan iska sun kai hari yankin gidan iyalan Saraki, sun raunata mutum 11
Yan iska sun kai hari yankin gidan iyalan Saraki, sun raunata mutum 11
Asali: Twitter

A cewar shugaban kungiyar ci gaban Agbaji, Alhaji Olanrewaju Yusuf, yan iskan sun samu jagorancin wani jigo na wata jam’iyyar adawa.

Yusuf yayi ikirarin cewa daya daga cikin wadanda aka kaiwa hari, dan shekara bakwai ya mutu.

Yace an dauki mutum 11 da suka samu rauni zuwa babbar asibiti, Ilorin da kuma wani asibitin kudi domin su samu kulawar likita.

An tattaro cewa daga bisani rikicin ya yadu zuwa yankunan Ajikobi da Omoda da ke garin Ilorin.

KU KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci

Darakta Janar na kungiyar kamfen din jam’iyyar PDP a jihar, Farfesa Suleiman Abubakar, yace shugabannin APC ne suka haddasa rikicin domin su tsoratar da mazauna yankin gabannin zabe.

Sakataren labaran PDP a jihar, Tunde Ashaolu, yace lamarin ya tabbatar da kiran da shugaban majalisar dattawa yayi akan barazana ga rayuwarsa.

Saraki yayi gaggawan dawowa Ilorin daga Erin-Ile da ke karamar hukumar Oyun da ke jihar Kwara inda yaje yin jawabi a wani gangamin siyasa.

Saraki a lokacin da ya ziyarci Agbaji, ya bukaci mutanensa da su kwantar da hankulansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel