APC na kara karfi a Gombe yayinda dan takarar gwamna a DPP, da daruruwan yan PDP suka sauya sheka

APC na kara karfi a Gombe yayinda dan takarar gwamna a DPP, da daruruwan yan PDP suka sauya sheka

- Jam’iyyar APC na kara yin karfi a jihar Gombe yayinda da zabe ke dada gabatowa

- A yanzu haka wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar DPP, Nafiu Bala Gombe da yan PDP 250 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar

- Nafiu wanda a kasance babban sakataren DPP na kasa yace ya yi murabus daga mukaminsa a jam’iyyar sannan ya koma APC saboda tsohuwar jam’iyyar tasa bata da alkibla

Yayinda guguwar zaben 2019 ke dada hurowa, yan takara da jam’iyyunsu na ci gaba da kokarin ganin sun samu karin magoya baya domin ganin sun kai labari, hakan ce ta kasance ga jam’iyyar APC a Gombe inda ake ganin tana kara yin karfi bayan wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar Democratic Peoples Party (DPP), Nafiu Bala Gombe ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Haka zalika akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne suka kaddamar da goyon bayansu ga APC a karamar hukumar Shongom.

APC na kara karfi a Gombe yayinda dan takarar gwamna a DPP, da daruruwan yan PDP suka sauya sheka

APC na kara karfi a Gombe yayinda dan takarar gwamna a DPP, da daruruwan yan PDP suka sauya sheka
Source: Depositphotos

Yayinda yake jawabi ga manema labarai akan ci gaban,sakataren labaran APC a jihar, Misis Naomi Joel Awak tace hakan ya karawa jam’iyyar farin jinni a jihar sannan ya nuna cewa jam’iyyar ta sirya kwace mulki a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Allura ta tono garma: An gano badakalar N500m da ake zargin Gamawa da hannu a ciki dumu-dumu

Da yake bayyana dalilansa a komawa APC, Nafiu Bala Gombe, wanda a kasance babban sakataren DPP na kasa yace ya yi murabus daga mukaminsa a jam’iyyar sannan ya koma APC saboda tsohuwar jam’iyyar tasa bata da alkibla.

Shugaban APC a jihar, Mista Nitte Amangal yayinda yake tarban mambobin PDP 25 zwa jam’iyyar a karamar hukumar Shongom ya bayyana cewa masu sauya shekar sun ga haske sannan a shirye suke da su kai Najeriya mataki na gaba da kuma chanja gwamnatin Gombe don samun inganci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel