Yanzu Yanzu: INEC ta gabatar da adadin masu zabe da aka yiwa rijista ga jam’iyyu siyasa

Yanzu Yanzu: INEC ta gabatar da adadin masu zabe da aka yiwa rijista ga jam’iyyu siyasa

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gabatar da adadin mutanen da aka yiwa rijistan zabe

- Adadin masu zabe da aka yiwa rijista su 84,004,084 (Miliyan tamanin dahudu, a dubu hudu da tamanin da hudu) ne

- An gabatar da adadwaanda aka yiwa rijistan ne a wani taron tattaunawa da jam’iyyun siyasa a Abuja

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya gabatar da adadin mutanen da aka yiwa rijistan zabe ga dukkan jam’iyun siyasa a zabe ai zuwa.

Legit.ng ta tattaro cewa adadin masu zabe da aka yiwa rijista su 84,004,084 (Miliyan tamanin da hudu, a dubu hudu da tamanin da hudu).

Yanzu Yanzu: INEC ta gabatar da adadin masu zabe da aka yiwa rijista ga jam’iyyu siyasa
Yanzu Yanzu: INEC ta gabatar da adadin masu zabe da aka yiwa rijista ga jam’iyyu siyasa
Asali: Facebook

An gabatar da adadwaanda aka yiwa rijistan ne a wani taron tattaunawa da jam’iyyun siyasa a Abuja.

A halin da ake ciki, kasa da makonni biyar kafin zaben kasar, INEC ta bayya cewa kimanin asu zabe miiyan takwas ne ba su karbi katunan zabensu ba ha yanzu.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Babban sakataren labaran Yahaya Bello ya yi murabus

Hakan na tattare ne a wani jawabi daga kwamishinan hukumar zabe na kasa, Mohammed Lecky, a okacin wani hira da jaridar THISDAY a ranar Asabar, 5 ga watan Janairu.

A wanilamari na daban, mun ji cewa Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zabe mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfen dinsa a Lokoja, babbar birin jihar Kogi a yau Litinin, 7 ga watan Janairu.

Mista Bode Ogunmola, kakakin jam’iyyar PDP a jihar Kogi kuma sakataren labarai na kungiyar kamfen din jam’iyyar a jihar, ne ya bayyana hakan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel