Manyan abubuwa 8 da suka faru a Kannywood a 2018

Manyan abubuwa 8 da suka faru a Kannywood a 2018

Shekarar 2018 ta kasance cike da lamura daban-daban ga dandalin wasan Hausa na Kannywood kama daga mai dadi, ban al’ajabi, bakin ciki da dai sauransu.

Wasu sun samu nasarori daban-daban a matakin gwamnati, sannan masu ruwa da tsakin dandanlin sun kara kaimi wajen inganta ayyukansu.

Hakan ya sa muka yi amfani da wannan damar wajen zakulo maku wasu daga cikin abubuwan da suka faru a dandalin.

1. Kano ta dage dakatarwan da ta yi wa Rahama Sadau

Shekarar ya kasance mai cike da farin ciki da walwala ga Rahama Sadau inda a watan Janairu ne Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya dage haramcin da aka sanya wa jarumar a masana’antar Kannywood, bayan kungiyar MOPPAN ta dakatar da ita a 2016 sakamakon wani bidiyon rawa da tayi da wani mawaki, Classique.

2. Adam Zango sun shirya da Ali Nuhu

Wannan shekarar ne aka shirya tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu tsohon ogansa, bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu. Shirin nasu na zuwa ne bayan da Aliyun ya ci kyautar Jarumai a taronsu na 'yan fim. Adam Zangon, yayi jinjina ga ogan nasa, inda ya kira shi da Sarki, kuma Oga, ya kuma taya shi murnar lashe kyautar.

3. Adam Zango ya sanya babban dansa a harkar waka

A shekarar nan ne kuma babban da ga fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa kuma mawaki watau Adam A. Zango mai suna Haidar Adam ya fitar da kundin wakokin sa na farko mai suna 'Take Over' bayan mahaifinsa ya shige masa gaba.

4. Mutuwar fitaciyyar jaruma Hauwa Maina

A shekarar 2018 ne kuma dai Allah ya yi wa shahararriyar yar wasar na Hauwa Maina rasuwa. Marigayiyar ta rasu ne a daren ranar Laraba, 2 ga watan Mayu a asibitin Malam Aminu Kano bayan tayi fama da rashin lafiya.

5. Ali Nuhu ya lashe kyautar Jarumai a taronsu na 'yan fim

Har ila yau a wannan shekarar ne fitaccen jarumin nan da tauraronsa ke ci gaba da hasakawa a masana’antar shirya fina-finan Ali Nuhu ya lashe kyautar Jarumai a taronsu na 'yan fim.

6. Bikin shahararren dan wasa kuma mawaki Ado Gwanja

A shekarar nan ne kuma aka sha shagalin bikin shahararren mawakin nan na Mata Ado Gwanja wanda aka fi sani da limamin mata, inda ya auri wata tsaleliyar budurwa mai suna Maimuna.

Bikin ya kuma samu halartan manyan jarumai da masu ruwa da tsaki a masana’antar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar matasan Arewa ta kaddamar da goyon baya ga shugaba Buhari

7. Mawaki Nazir Ahmad ya zama mawakin sarkin Kano

A watan Nuwamban wannan shekarar ne dai aka sanar da zabar mawakin Kannywood, Nazir Ahmad a matsayin mawakin sarkin Kano, sannan kuma ranar 27 ga watan Disamba ne Sarki Sanusi ya nada masa sarauta a masarautarsa ta Kano.

8. Soyayyar Atiku da Buhari ya raba kan yan Kannywood

Sakamakon kadowar guguwar siyasa a samu rabuwar kai Kannywood inda wasu jarumai ke goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 yayinda wasu kuma ke goyon bayan Atiku Abubakar. Koda dai yan wasan sun karyata samun rabuwar kai a tsakanin nasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel