Buhari zai kashe N7.3bn kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019

Buhari zai kashe N7.3bn kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019

- Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira bilyan 7.30 wajen hada-hadar shan mai da kula da jiragen zirga-zirgar Shugaba Buhari a shekarar 2019

- Bayanan yadda za a kashe wadannan makudan kudaden na kunshe a daftarin kasafin kudin wannan shekarar da aka hgabatar a kwanakin baya

- Cikin kasafin da aka ware wa jiragen, har da batun sake kayan dafe-dafen abinci, sake inganta karfin intanet da sauran su

Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira bilyan 7.30 wajen hada-hadar shan mai da kula da jiragen zirga-zirgar Shugaba Muhammadu Buhari a cikin shekarar 2019, jaridar Premium Times ta rwaito.

Bayanan yadda za a kashe wadannan makudan kudaden na kunshe a daftarin kasafin kudin 2019 da aka ware domin kashe wa Buhari a zirga-zirgan da jiragensa za su yi a ciki da wajen Najeriya.

Buhari zai kashe N7.3bn kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019

Buhari zai kashe N7.3bn kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019
Source: UGC

Wannan adadi na nuna cewa abin da jirgin Buhari zai kashe a 2019, ya haura adadin da aka kashe a shekarar 2017 da kuma 2018.

Cikin kasafin da aka ware wa jiragen, har da batun sake kayan dafe-dafen abinci, sake inganta karfin intanet da sauran su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019

Jiragen Shugaban Kasa su ne jirage na biyu mafi yawa a Najeriya.

Sannan kuma ana ta korafin yadda ake kashe makudan kudade a kan jirgin, fiye ma da lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel