Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci

Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci

- Wani magidanci ya harbe matarsa da yaransa biyu har lahira, inda ya zarge ta da kafircewa

- Al’amarin ya faru ne a kauyen Ovbiogie a karamar hukumar Obia ta arewa maso gabas da ke jihar Edo

- Kwamishinan yan sanda a jihar, Mr Hakeem Odumosun, wanda ya ziyarci wajen afkuwar lamarin, yayi alkawarin cewa za a mika mai laifin gaban kotu bayan an kammala bincike a cikin lamarin

Wani mutum mai hekara 35 a duniya, da aka ambata da suna Uwaila, a ranar Lahadi ya harbe matarsa da yaransa biyu har lahira a Edo, inda ya zarge ta da kafircewa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a kauyen Ovbiogie a karamar hukumar Obia ta arewa maso gabas da ke jihar.

Kwamishinan yan sanda a jihar, Mr Hakeem Odumosun, wanda ya ziyarci wajen afkuwar lamarin, yayi alkawarin cewa za a mika mai laifin gaban kotu bayan an kammala bincike a cikin lamarin.

An tattaro cewa mai laifin yayi harbi ta kofa zuwa cikin dakin da matar da yaran suka shige don tsira bayan sun rufe kansu, sakamakon wani sainsa da ya shiga tsakaninsu.

Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci
Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci
Asali: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta kuma ruwaito cewa mazauna garin koka ba da wasa ba a lokacin da jami’an hukumar hana afkuwar hatsarurruka suka kwashe gawawwakin.

Da yake bayanin abunda ya faru, mai laifin wanda ke a hannun yan sanda, yace matarsa ta zarge shi da hulda da yan mata sannan tayi zargin za ta rama ta hanyar bin maza.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoro a Borno yayinda Boko Haram suka kai hari Magumeri

Uwaila yace ya bar gidan cikin bacin rai sannan ya dawo ya tarar matar ta rufe kanta da ‘ya’yansa a daki daya.

Yace sai yayi harbi ta kofa, inda ya kara da cewa a wannan halin ne sai harsashi ya same su akan gado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel