Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

- Uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Hajiya Titi Atiku Abubakar, ta roki yan Najeriya da su yi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa

- Hajiya Titi ta yi zargin cewa gwamnatin Buhari ta rasa hanyarta

- Uwargidan Atiku ta kuma ce shugaba Buhari bai da ilimin tattalin arziki don haka bai cancanci zarcewa ba

Hajiya Titi Atiku Abubakar, uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ta roki yan Najeriya da su yi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, cewa gwamnatinsa ta rasa hanyarta.

Misis Abubakar ta yi wannan furucin neyayinda take jawabi a wani taro a Najeriya mai taken : ‘Kick Out Hunger, Kick Out APC’ wato ayi waje da yunwa, ayi waje da APC, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa uwargidan Atiku ta nuna adawa da nadin Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin hada sakamakon zabe, cewa “Bama son Amina Zakari a dakin tattara kuri’u.”

Tace kada yan Najeriya su bari shugaba Buhari ya samu damar zrcewa, domin guje ma durkushewar kasar. A cewar Misis Abubakar, shugaban kasar bai da ilimin tattalin arziki.

KU KARANTA KUMA: Shugaban PDP a cikin Jihar Kebbi ya sauya-sheka zuwa APC

Taron ya kuma samu halartan matayen manyan shugabannin PDP, ciki harda Misis Toyin Saraki, uwargidan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Misis Gimbiya Yakubu Dogara, uwargidan kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel