Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro

Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro

- Sojojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram sama da 280 a kusa da iyakar kudu maso gabas da Najeriya a kwanakin da aka yi ana kai mamaya ta kasa da sama

- Mayakan Boko Haram 200 rundunar sojin suka kashe ta sama yayinda aka sake kashe wasu 87 ta kasa tun da aka fara aikin

- An kwace kwale-kwale takwas da roka biyu da kuma makamai, alburusai da ababen hawa

Rundunar sojin kasar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram sama da 280 a kusa da iyakar kudu maso gabas da Najeriya a kwanakin da aka yi ana kai mamaya ta kasa da sama, cewar ma’aikatar tsaro a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu.

Ma’aikatar ta bayyana a wani jawabi da ya saki cewa sama da mayakan Boko Haram 200 rundunar sojin suka kashe ta sama yayinda aka sake kashe wasu 87 ta kasa tun da aka fara aikin a ranar 28 ga watan Disamba.

Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro

Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro
Source: UGC

Hakan na zuwa ne bayan shugabannin kasashen Afrika ta yamma sun gudanar da tattaunawa a Nuwamba kan hare-haren da yan ta’addan na Najeriya ke kaiwa a yankin tafkin Chadi, inda iyakokin Chadi, Kamaru, Najeriya da Nijar suka hade.

An gudanar da ayyukan ne a tsibirin tafkin Chadi da kuma hanyar kogin Komadougou Yobe wanda ya kasance iyaka tsakanin Nijar da Najeriya, wanda yayi fama da hare-hare a sansanonin sojojinta a yan kwanakin nan.

KU KARANTA KUMA: Na samu gagarumn nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

Rundunar sojin Nijar basu rasa kowani jami’i ko kayan aiki ba a harin sannan sun kwace kwale-kwale takwas da roka biyu da kuma makamai, alburusai da ababen hawa.

A watan Disamba, ministan tsaroin Nijar yace yayi tsoron ko Boko Haram za su sabonta har-hare daga watan Janairu lokacin da kogin Komadougou Yobe wanda ke hana su kai hari ya fara ja da baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel