Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019

Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019

- Kungiyar fararen mayu a Najeriya sun ce Atiku zai iya lashe zabe bisa sharadi guda

- Mayun sun gargadi Atiku da ya bi shawarar manya don kada ya yi irin kuskuren da Jonathan yayi a 2015

- Sun kuma gargadi INEC da kada ta bari ayi amfani da ita wajen yin magudi a zabe

Kungiyar fararen mayu a Najeriya ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da za a yi, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kada ya maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a 2015, idan har yana son ya lashe zabe.

A cewar mayun, Jonathan ya ki sauraron shawarar masu hikima wanda hakan ne ya sa shi shan kaye a zaben 2015 inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben.

Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019
Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019
Asali: Facebook

Kungiyar ta gargadi Atiku da ya dauki sharudan da aka gindaya masa idan har yana son yayi nasara a zabe mai zuwa sannan ya fitar da yan Najeriya daga yunwa da talauci wanda mumunan manufar tattalin arziki na wannan gwamnati ya jefa su a ciki.

Daily Independent ta ruwaito cewa kakakin kungiyar, Okhue Iboi, wanda yayi magana a wani hira na wayar tarho a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu yace ya zama dole Atiku ya dunga ziyarar coci, masallaci da kungiyar mayu domin addu’o’i na musamman idan har yana son yin nasara.

KU KARANTA KUMA: Bakare ya yi magana game da zama shugaban kasar Najeriya na 16 (bidiyo)

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta fadi zaben gwamna a jihar Ogun idan hart bata ba Sanata Buruji Kashamu tikitin takara ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel