Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato garin Baga na jihar Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato garin Baga na jihar Borno

- Rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar kwace iko da garin wanda a baya ya koma karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram

- Sojin sun kutsa kai cikin garin na Baga a yammacin ranar Laraba, 9 ga watan Janairu inda suka fatattaki yan ta’addan

- Hakan na zuwa dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai fiye da mutane dubu 30 da yanzu haka su ka fice daga garin na Baga don kaucewa mulkin Boko Haram bayan da ta kwace iko da garin

Rahotanni daga garin Baga na jihar Borno sun nuna cewa yanzu haka jami'an rundunar sojin kasar sun yi nasarar kwace iko da garin wanda a baya ya koma karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya rahoto cewa dakarun sojin sun kutsa kai cikin garin na Baga a yammacin ranar Laraba, 9 ga watan Janairu inda suka fatattaki yan ta’addan.

Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato garin Baga na jihar Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato garin Baga na jihar Borno
Source: Facebook

Matakin sake kwace iko da garin na Baga na zuwa dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai fiye da mutane dubu 30 da yanzu haka su ka fice daga garin na Baga don kaucewa mulkin Boko Haram bayan da ta kwace iko da garin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu

Wasu hare-haren mayakan na Boko Haram kan sansanonin sojin Najeriyar a Baga cikin makwannin da suka gabata wanda suka kai ga kisan da dama ne ya bai wa Boko Haram damar kwace iko da garin.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa da misalin karfe 5 da rabi na yammaci lokacin da ya ke kokarin yin hijira daga garin ya ga jerin gwanon motocin sojoji sun yi wa garin tsinke, inda kai suka yi sansani a Kuros-Kauwa mai tazarar kilomita 15 kafin afkawa Baga da misalin karfe 7 na dare.

"A hankali sojojin Najeriya sun sake karbe Baga, Koruskauwa sannan suna dada fatattakan yan ta’addan Boko Haram daga arewa.

"Idan har za a cigaba da samun irin wannan galabar muna iya soke yan Boko Haram cikin sauki," cewar shahararren dan jaridar nan Ahmad Salkida yayinda yake tabbatar da nasarar rundunar sojin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel