2019: Buhari na yaudarar Tinubu ne kawai - Afenifere

2019: Buhari na yaudarar Tinubu ne kawai - Afenifere

- Kungiyar ta Yarbawa ta Afenifere, ta bayyana cewa hukuncin Shugaba Buhari na neman Tinubu ya jagoranci tawagar kamfen dinsa, ba komai bace face yaudara

- Kakakin Afenifere, Yinka Odumakin, ya kuma ce nada Tinubu a matsayin tawagar kamfen din na iya yiwuwa shugaba Buhari na neman hanyar guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa

- Ya bukaci Buhari da ya gaggauta canja tunanin sa game da halartar muhawarar domin yan Najeriya ba za su zabi duk wanda yaki halartan muhawararba

Wannan kungiyar ta Yarbawa wato Afenifere, ta bayyana cewa hukuncin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya jagoranci tawagar kamfen dinsa, ba komai bace face yaudara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin Afenifere, Yinka Odumakin, ya kuma ce nada Tinubu a matsayin tawagar kamfen din na iya yiwuwa shugaba Buhari na neman hanyar guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa.

2019: Buhari na yaudarar Tinubu ne kawai - Afenifere

2019: Buhari na yaudarar Tinubu ne kawai - Afenifere
Source: UGC

Yinka Odumakin ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da maneman labarai inda ya ce matsayin jagoran kamfen yakin neman zaben da Shugaba Buharin ya ba Tinubu ba zai zamo masa mafaka ba.

KU KARANTA KUMA: Faifan murya: Atiku ya bukaci Aaechi da ya dawo PDP kafin zabe

Sai dai kuma kakakin na kungiyar Afenifere ya kara da ba shugaba Buhari shawarar kan ya gaggauta canja tunanin sa game da halartar muhawarar domin yan Najeriya ba za su zabi duk wanda yaki halartan muhawararba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel