Allura ta tono garma: An gano badakalar N500m da ake zargin Gamawa da hannu a ciki dumu-dumu

Allura ta tono garma: An gano badakalar N500m da ake zargin Gamawa da hannu a ciki dumu-dumu

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa ana zargin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Babayo Gamawa, wanda jam’iyyar ta dakatar, shi kuma ya koma APC, da rarumar kudade har naira miliyan 500.

Hukumar yaki da cin hanci da ana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) na binciken batar kudaden a hannun sa ba tun yau ba, kuma har ma an gurfanar da shi a kotu.

Ana zargin Gamawa ne tare da wasu mutane biyar a Bauchi da zargin karbar naira miliyan 500 na kudin kamfen a cikin 2015 lokacin ya na PDP.

EFCC ta ce kudaden na daga cikin makudan kudaden da tsohuwar ministan man fetur Diezani Allison-Madueke ta dunga rabawa domin kamfen din 2015.

Allura ta tono garma: An gano badakalar N500m da ake zargin Gamawa da hannu a ciki dumu-dumu
Allura ta tono garma: An gano badakalar N500m da ake zargin Gamawa da hannu a ciki dumu-dumu
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hukumar ta EFCC ta gurfanar da Gamawa a Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi, a cikin watan Yuni, 2018.

Gamawa ya koma jam’iyyar APC jiya Talata, bayan PDP ta dakatar da shi, bayan an yi masa zargin rashin gudanar da aikin sa, da kuma yi wa PDP zagon-kasa.

KU KARANTA KUMA: Tsoron hukunci ne ya sa Gamawa guduwa APC – Yakassai

Gwamnan Jihar Bauchi, Abubakar Mohammed ne ya kai shi wurin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya i murna sosai da komawar da ya yi cikin APC, jam’iyyar Buhari mai yaki da cin hanci da rashawa.

Da dama na ganin cewa goya Gamawa da Buhari ya yi, tamkar abin da Hausawa ke kira tsaftar biri ne, wai kashi a cikin moda.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel