Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya cika Shekaru 20 a masana’antar shirya fina-finan Hausa

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya cika Shekaru 20 a masana’antar shirya fina-finan Hausa

- Jarumin jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim

- Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999

- Tauraronsa na ci gaba da haskawa a masana'antar duk da tsawon shekarun nan da ya dauka yana harkar

Shahararren jarumin nan da yaga jiya yaga yau a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim.

Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999.

Jarumin ya samu tarin nasarori kama daga lambar yabo da dama, da kuma tarin daukaka bama a arewacin kasar kawai ba, harma ga sauran sassan kasar dama duniya baki daya.

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya cika Shekaru 20 a masana’antar shirya fina-finan Hausa
Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya cika Shekaru 20 a masana’antar shirya fina-finan Hausa
Asali: Twitter

Tun a zamanin da ya fara fitowa a wasanni tauraronsa ke haskawa inda aka yi ittifakan babu wanda ya kais hi farin jini a masana’antar gabaki daya kama daga wadanda suka fara harkar tare har zuwa ga wadanda ke tasowa a yanzu.

Hakan ya sanya ake yi masa inkiya da sarki mai Kannywood. Sai dai hasashe sun nuna cewa sirrin daukakarsa na daga hazaka da kokarin jarumin akan sana’arsa, sannan kuma shi din mutum ne mai son ganin ci gaban wadanda ke tasowa a masana’antar.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

Ya kuma zamo silar shigowar mutane da dama masana’antar, sannan kuma ya zamo silar daukakarsu. Cikin irin wadanna mutane da ya kawo akwai Rahama Sadau wacce tauraronta ke haskawa, da kuma Maryam Yahaya da dai sauransu.

Muna taya jarumin murnar wannan tafiya mai nisa da yayi a rayuwarsa!

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel