Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Kwamishinan yan sandan jihar Ondo, Bolaji Salami, ya tabbatar da mutuwar yan sanda biyu da wani dan farar hula daya a rikicin da aka yi a makon da ya gabata.
A yayinda ake ci gaba da sace-sace da lalata kayayyaki a yankuna daban-daban na kasar, bata gari sun sace madubin idon da ke sanye a idanun gunkin Awolowo.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon Gwamnan Jihar Legas a lokacin mulkin soja, Mohammed Buba Marwa bisa rasuwar dan uwansa.
Wasu bata gari karkashin fakewa da zanga-zangar #EndSARS sun fasa shagunan mutane a garin Kano ciki har da shagon Mansura Isah, tsohuwar jarumar Kannywood.
Wasu matasa da ake zaton bata gari ne sun balle wani dakin aiyar kayan abinci mai zaman kansa a yankin Madalla da ke jihar Niger, sun wawure kayan da ke ciki.
Masu yawon neman wajen da aka ajiye kayan tallafin korona sun bazama cikin unguwanni a yankin Kuje a babbar birnin tarayya Abuja, hakan ya haifar da fargaba.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bukaci kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood da mawaka su fadakar da jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.
Dakarun sojojin Najeriya sun lallasa yan ta'addan Boko Haram a yayinda suka yi yunkurin kai hari sansaninsu na Damboa, jihar Borno sun halaka 16 daga cikinsu.
Rahoto ya nuna cewa tashin hankali ya barke a yankin Abakaliki, wato babbar birnin jihar Ebonyi, yayinda wasu bata gari suka cinna wa ofishin yan sanda a wuta.
Aisha Musa
Samu kari