Abun dariya abun haushi: An sace madubin idon gunkin Awolowo a Lagos

Abun dariya abun haushi: An sace madubin idon gunkin Awolowo a Lagos

- Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a sassa daban-daban sakamakon zanga-zangar EndSARS da matasa suka yi a kasar

- Bata gari dai sun zage damtse sai sace-sacen kayayyaki suke tare da fashe-fashen kayan gwamnati

- Hatta da mutum-mutumin Obafemi Awolowo bai tsira ba a wannan harin domin a yanzu haka an sace madubin idon da gunkin nasa ke sanye da shi

Kwanaki bakwai bayan gwamnatin Lagas ta kaddamar da dokar kulle domin hana sace-sace da barna a fadin jihar, har yanzu ba a ga madubin idon gunkin Obafemi Awolowo ba a yankin Ikeja, jaridar The Cable ta ruwaito.

Bata gari dai sun janye ragamar zanga-zangar EndSARS a jihar, lamarin da ya haddasa barkewar rikici inda aka yi ta lalata kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kansu.

An lalata motoci, na’urar cire kudade na banki da sauransu, hatta da gunkin Awolowo bai tsira ba a yayinda ake sace-sacen, domin har yanzu ba a ga madubin idonsa ba.

Abun dariya abun haushi: An sace madubin idon gunkin Awolowo a Lagos
Abun dariya abun haushi: An sace madubin idon gunkin Awolowo a Lagos Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: Ganduje ya gabatar da wata muhimmiyar bukata a gaban Rarara da Ali Nuhu

An san Awolowo, wanda ya kasance firam ministan yankin kudu daga 1954 zuwa 1960, da kayataccen madubin idonsa wanda yake mulmulalle.

A watan Satumba 2017 ne Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan jihar Lagas, ya bayyana gunkin na Awolowo mai tsawon sahu 20 a hanyar Obafemi Awolowo kusa da mahadin hanyar LTV a Ikeja.

Ambode ya ce an kafa gunkin ne domin karrama nasarori da gudunmawar da Awolowo ya bayar wajen ci gaban kasar.

A wani labarin kuma, wasu matasa da ake zaton bata gari ne a birnin Kano, sun kai mamaya shagon tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa da ke jihar.

Bata garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka yashe komai da ya ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

Mansura wacce ta kasance mata ga fitaccen jarumin masana’antar, Sani Musa Danja, ce ta wallafa bidiyo da hotunan shagon da aka fasa mata a shafinta na Instagram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel