Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno

Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno

- Hazikan sojoji sun yi nasarar dakile wani hari da yan ta'addan Boko Haram suka yi yunkurin kai wa sansaninsu a garin Damboa

- Yan ta'addan sun halaka yan gudun hijira hudu tare da jikkata wasu 10

- Sai dai kuma suma sun dandana kudarsu a hannun soji, inda 16 daga cikinsu suka halaka

Akalla mutane 20 ciki harda yan Boko Haram 16 aka kashe, a lokacin da yan ta’addan suka yi yunkurin kai hari wani sansanin sojoji a yankin kudancin jihar Borno, a yammacin ranar Lahadi, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

An tattaro cewa maharan sun isa garin Damboa, hedkwatar karamar hukumar Damboa da ke jihar, sannan suka bude wuta inda suka kashe yan gudun hijira hudu.

Har ila yau, wasu mutane 10 sun jikkata a yayin bude wutar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno
Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno Hoto: TRT World
Asali: UGC

Wata babbar majiya ta tsaro, ta bayyana cewa yan ta’addan sun kaddamar da wani hari kan sansanin sojoji amma sai suka hadu bacin rana sannan aka kashe 16 daga cikinsu.

KU KARANTA KUMA: Lekki: Femi Falana ya ce sun fara bincike, sun nemo barikin sojojin da su ka yi harbe-harbe

Majiyar ta kara da cewa an kwashi kimanin sa’o’i uku ana musayar wutan sannan rundunar sojin sama Operation Lafiya Dole suka taimaka rundunar sojin kasa wajen lallasa yan ta’addan.

“Ina iya fada maka cewa ba a rasa rai ko guda ba daga bangarenmu. Daga dakarun sojin sama har na kasa sun yi namijin kokari,” in ji majiyar tsaron.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Fafaroma Francis ya ce ayi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya

Wani dan kungiyar yan banga a Damboa, Hamisu Bakura, ya fada ma jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa “Boko Haram sun zo da motocin bindigogi fiye da 20, sannan suka yi ta harbi ta ko’ina.

“Kowa na ta gudu sannan harbin ya samu yan gudun hijira su uku inda suka mutu. Wani ya sake rasa ransa a asibiti don haka yan gudun hijira hudu kenan muka rasa amma muna farin ciki da ganin cewar an kashe yan Boko Haram da yawa. A yanzu haka da muke magana ana biki a Damboa."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel