Sun ji uwar bari: Ɓata gari sun fara maido da kayan da suka sata a Adamawa
- Wasu bata gari da suka yi sace-sace a rumbunan gwamnati da na daidaikun mutane a Adamawa sun fara dawo da kayayyakin da suka sata
- Gwamna Ahmad Fintiri a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, ya roki bata garin a kan su dawo da kayayyakin satan
- Fintiri ya yi barazanar cewa zai tabbatar da hukunta wadanda suka ki bin umurnin
Yan sa’o’i bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya aika sakon gargadi zuwa ga bata garin da suka yi sace-sace a rumbunan ajiya a Adamawa, wasu da suka yi satan sun fara dawo da kayayyakin da suka sata domin tsiratar da kansu daga hukunci mai tsanani.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan ya yi barazanar cewa zai rushe gidajen da aka samu kayayyakin satan a ciki.
KU KARANTA KUMA: 2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

Asali: Twitter
Legit.ng ta tattaro cewa rahoton ya nuna cewa wasu mazauna Yola da Jimeta sun fara dawo da kayayyakin da suka sata zuwa ga masu unguwanninsu yayinda wasu suka ajiye a kan hanyoyi domin mahukunta su dauka.
A cewar jaridar, wasu daga cikin kayayyakin da aka dawo da su sun hada da firinji, kayayyakin inin noma, famfuan ruwa, kayan kujeru, kayan asibiti da buhuhunan taki.
A baya mun ji cewa, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce duk wanda ya san ya saci kayan tallafin COVID-19, yayi gaggawar mayarwa cikin awanni 12.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata, yayin gabatar da jawabi ga jama'an jihar Adamawa.
A cewarsa, "Na bai wa duk wadanda suka saci kayan abinci daga ma'adanar gwamnati daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe, su yi gaggawar mayar da kayan abincin ga ofishin 'yan sanda mafi kusa da su."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng