Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje

Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje

- A yanzu haka wasu bata gari sun bazama cikin garin Kuje suna neman rumbun ajiyar kayan tallafin korona

- Lamarin ya haddasa fargaba da tsoro a zukatan al'umma yayinda yan kasuwa suka rufe shagunansu don gudun barkewar rikici

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke ci gaba da fashe-fashen wurare suna sace-sace a sassa da dama na kasar

Jama’a sun shiga halin fargaba a yankin Kuje, daya daga cikin kananan hukumomi shida da ke babbar birnin tarayya. Hakan ya biyo bayan yawon da wasu bata gari ke yi suna neman rumbun ajiye kayan tallafin korona domin sace su.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa bata garin sun bazama unguwa-unguwa dauke da sanduna, sannan suna ta toshe hanyoyi a cikin garin Kuje.

An tattaro cewa mazauna yankin na tserewa domin neman mafaka yayinda yan kasuwa ke rufe shagunansu sannan suna ta barin kasuwar don gudun barkewar rikici.

Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje
Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: Ganduje ya gabatar da wata muhimmiyar bukata a gaban Rarara da Ali Nuhu

A ranar Litinin, mutum uku ne suka mutu sakamakon turereniya lokacin da bata gari suka fasa rumbun aiye kayan tallafin kororna na Gwagwalada sannan suka kwashe kayan abinci da sauran muhimman abubuwan da ke ciki.

A yanzu haka jami’an tsaro da suka hada da sojoji da yan sanda na kokarin ganin sun daidaita lamarin.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno

A baya mun ji cewa jama’a da ke yawon neman wajen da aka ajiye kayan tallafin korona sun kai farmaki wani rumbun ajiye kaya a Gwagwalada, babbar birnin tarayya, Abuja.

Kayayyakin da suka sace sun hada da shinkafa, semovita, taliya, siga, gishiri da taki.

Rumbun ajiyar wanda ke kusa da ofishin WAEC, an tattaro cewa yana dauke da kayayyaki mallakar hukumar birnin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel