Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

- Bata gari sun fasa shagunan mutane a garin Kano ciki har da shagon tsohuwar arumar Kannywood, Mansura Isah

- Matasan wadanda suka fake da zanga-zangar EndSARS sun kwashe komai da ke ciki shagon jarumar

- Mansura ta bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan sun hade kayayyakin dukka shagunansu a waje daya

Wasu matasa da ake zaton bata gari ne a birnin Kano, sun kai mamaya shagon tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa da ke jihar.

Bata garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka yashe komai da ya ke ciki.

Mansura wacce ta kasance mata ga fitaccen jarumin masana’antar, Sani Musa Danja, ce ta wallafa bidiyo da hotunan shagon da aka fasa mata a shafinta na Instagram.

Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai
Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai Hoto: mansurah_isah
Asali: Instagram

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje

Ta wallafa a shafin nata cewa “Mun tattara kayanmu da ke ragowar sauran ofishinmu da ke unguwar Badawa zuwa wuri daya domin rage wa kanmu wahala akoda yaushe ta hanyar zirga-zirga daga wannan shagon zuwa wancan. Ofishinmu na @todays_life_foundation da ke Badawa layout, da shagonmu na daukar hoto @celebrityphotos2442 da kuma tsohon shagona da ke Audu Bako.

“Mun kwashe komai da ya ke shagon kama daga Takalma, jakunkuna, Firji, AC, Talabin da sauran kayayyaki daga tsoffin shagunan zuwa wannan sabon shagon domin mamallakan shagunan sun bukaci mu bar masu wajensu tunda ba za mu sake biyan haya ban a wata shekarar.

Amma sunsace komai, basu bar ko takalmi daya ba. Sun kwashe komai da komai. Amma mun fawwala wa Allah komai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

“Dama mun san mutane suna neman dama irin wannan ne domin su aikata mummunan laifuka, sun fake da zanga-zangar #EndSARS da kuma #EndInsecurity don su lalata dukiyoyin jama’a da rayukan mutane.”

"Amma ina addu’a ga samun sabuwar Najeriya kuma muna yi wa kasarmu addu’an samun zaman lafiya. Alhamdulillah da kasancewa da lafiya da rayuwa.”

A gefe guda, Abdullahi Ganduje, a kokarin da yake na ganin an samu zaman lafiya a Kano, ya roki kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da na mawaka a kan su yi amfani da kwarewarsu wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaman lafiya.

Ya yi wannan kira ne a yayin wata ganawa da ya yi da kungiyar MOPAN a ranar Talata, a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel