Yanzu Yanzu: Rikici ya sake barkewa a Abakaliki

Yanzu Yanzu: Rikici ya sake barkewa a Abakaliki

- Rikici ya sake barkewa a yankin Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi

- An tattaro cewa wasu bata gari sun sanya wa ofishin yan sanda da ke Onuebonyi wuta

- A yanzu haka ance ana nan ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da bata garin

Labari da ke zuwa mana, ya nuna cewa rikici ya sake barkewa a garin Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi yayinda ake ta ruwan harbi a sama.

Rikicin wanda ya fara kimanin sa’a guda da ta gabata ya haifar da fargaba a birnin yayinda mazauna suka tarwatse ta kowani bangare, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa ba a san daga takamaiman wurin da harbe-harben bindigar ke fitowa ba.

KU KARANTA KUMA: Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje

Yanzu Yanzu: Rikici ya sake barkewa a Abakaliki
Yanzu Yanzu: Rikici ya sake barkewa a Abakaliki Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Sai dai kuma rahoton yanar gizo ya nuna cewa wasu bata gari sun cinnawa ofishin yan sanda na Onuebonyi wuta.

An kuma rahoto cewa jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro na nan suna musayar wuta da bata garin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: Ministocin Buhari 2 sun mika kokon bararsu a gaban Sarkin Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan daba a safiyar ranar Lahadi, sun kai farmaki ofishin yan sandan Mokola da ke Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, a kokarinsu na son kona ofishin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sai da matasan yankin suka shiga lamarin kafin aka iya hana yan daban kona ofishin yan sandan.

Daya daga cikin matasan da ke makwabtaka wadanda suka hana yunkurin kona ofishin, Musa Muhammed, ya bayyana cewa saura kadan a kashe wata inspekta mace.

Ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban matasa shine ya tara mutane suka dakile harin yan daban na kona ofishin yan sandan.

Ya kuma bayyana cewa rikicin ya fara ne dokacin da harbin bindiga ya kashe wani yaro da bai ji ba bai gani ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel