Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

- Matasa sun ɓalle dakin ajiyar kayan abinci a yankin Madalla da ke jihar Niger

- Tuni dai matasa suka fara wawason kayayyakin bayan sun samu shiga rumbun ta hanyar haura katanga

- An tura jami'an tsaro wajen domin taka masu birki

Rahotanni daga garin Madalla a jihar Neja ya nuna cewa, wasu daruruwan matasa sun kai mamaya wani dakin ajiya mai zaman kansa, mallakar wani dan Labanon a yankin.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, matasa sun mamaye kamfanin wacce a baya aka sani da Madalla Floor Mill wanda ke a hanyar titin Abuja/Kaduna tun da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Talata, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa sun yi nasarar shiga kamfanin ta hanyar haura katanga.

Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso
Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

An mayar da kamfanin Madalla Floor Mill zuwa dakin ajiyar kaya kwanakin baya inda yan kasuwa daga Suleja da sauran yankuna ke adana kayayyakinsu.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: Ganduje ya gabatar da wata muhimmiyar bukata a gaban Rarara da Ali Nuhu

An bunkasa aikin ajiyar zuwa ga kungiyoyin hadin gwiwa, gwamnati da yan siyasa.

An bayyana cewa an adana kayayyakin tallafin gaggawa a wajen a lokacin kullen korona.

An kuma tattaro cewa da misalin karfe 10:00 na safe, matasan sun fara fita da kayayyakin da aka ajiye a rumbun, a yayinda jami’an tsaro da aka zuba a wajen keta harbi a sama.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno

A gefe guda, jama’a sun shiga halin fargaba a yankin Kuje, daya daga cikin kananan hukumomi shida da ke babbar birnin tarayya. Hakan ya biyo bayan yawon da wasu bata gari ke yi suna neman rumbun ajiye kayan tallafin korona domin sace su.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa bata garin sun bazama unguwa-unguwa dauke da sanduna, sannan suna ta toshe hanyoyi a cikin garin Kuje.

An tattaro cewa mazauna yankin na tserewa domin neman mafaka yayinda yan kasuwa ke rufe shagunansu sannan suna ta barin kasuwar don gudun barkewar rikici.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel