Buhari ya aike da saƙon ta'aziyya ga Janar Buba Marwa ta mutuwar ɗan uwansa

Buhari ya aike da saƙon ta'aziyya ga Janar Buba Marwa ta mutuwar ɗan uwansa

- Shugaba Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Jigon APC, Birigediya Janar Buba Marwa bisa rasuwar dan uwansa

- Alhaji Idris Marwa mai shekara 57 a duniya ya rasu ne bayan gajeriyar rahsin lafiya

- Buhari ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin tare da ba iyalansa juriya da dangana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, ya mika ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Lagas a mulkin soja kuma jigon APC, Birgediya Janar Buba Marwa, kan mutuwar kaninsa, Idris.

Buhari ya aika ta’aziyyar ne a cikin wata sanarwa da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ya saki.

Alhaji Idris Marwa, wanda ya kasance babban dan kasuwa a Kaduna ya rasu a ranar Talata, bayan yar gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 57 a duniya, jaridar PM News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

Buhari ya aike da saƙon ta'aziyya ga Janar Buba Marwa ta mutuwar ɗan uwansa
Buhari ya aike da saƙon ta'aziyya ga Janar Buba Marwa ta mutuwar ɗan uwansa Hoto: @thesunnigeria
Asali: Twitter

Da yake ta’aziya ga iyalan Marwa, Shugaban kasar ya bukace su da su dauki dangana domin dukkan mai rai mamaci ne zai koma ga mahaliccinsa.

“Abun da ya fi muhimmanci shine yadda muka tafiyar da ayyukanmu a nan gidan duniya, kuma na yarda cewa Idris Marwa ya taka rawarsa da kyau.”

Shugaban kasar ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin, Ya kuma yi masa rahama, sannan ya ba abunda ya bari a baya juriyar wannan babban rashi.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

A wani labari na daban, akalla mutane 20 ciki harda yan Boko Haram 16 aka kashe, a lokacin da yan ta’addan suka yi yunkurin kai hari wani sansanin sojoji a yankin kudancin jihar Borno, a yammacin ranar Lahadi, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

An tattaro cewa maharan sun isa garin Damboa, hedkwatar karamar hukumar Damboa da ke jihar, sannan suka bude wuta inda suka kashe yan gudun hijira hudu.

Har ila yau, wasu mutane 10 sun jikkata a yayin bude wutar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel