Zanga-zanga: Ganduje ya gabatar da wata muhimmiyar bukata a gaban Rarara da Ali Nuhu
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya tunkari masana'antar shirya fina-finai domin su taimaka masa wajen tabbatar da zaman lafiya a jiharsa
- Ganduje ya nemi Rarara da Ali Nuhu su yi amfani da kwarewarsu wajen shirya fim da yin wakar wayar da kai ga al'umma don jadadda masu muhimmancin zaman lafiya
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a kokarin da yake na ganin an samu zaman lafiya a jihar, ya roki kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da na mawaka a kan su yi amfani da kwarewarsu wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaman lafiya.
Ya yi wannan kira ne a yayin wata ganawa da ya yi da kungiyar MOPAN a ranar Talata, a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin jihar, jaridar Aminiya ta ruwaito.
A cikin jawabin nasa, gwamnan ya yi kira ga shahararren mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, a kan ya rera wakokin wayar da kai ga jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.
KU KARANTA KUMA: Boko Haram: An kashe mutum 20 yayinda aka jikkata 10 a jihar Borno
Har ila yau, ya bukaci fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, da ya shirya fina-finan wayar da kan al’umma kan fa’idar zaman lafiya.
Ana dai ta fuskantar rashin zaman lafiya a wasu jihohin kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS da aka fara gudanar da ita makonni biyu da suka gabata.
KU KARANTA KUMA: Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso
A gefe guda, mun ji cewa, an yi kira ga sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a kan ya sanya baki domin kawo karshen zanga-zangar da matasa ke yi a jihar.
Ministan tsaro, Bashir Magashi da takwaransa na noma, Sabo Nanono, wadanda suka kasance yan asalin jihar ne suka yi wannan kira.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng