Yanzu Yanzu: An kashe jami’an yan sanda 2, da dan farar hula 1 a rikicin Ondo

Yanzu Yanzu: An kashe jami’an yan sanda 2, da dan farar hula 1 a rikicin Ondo

- Jami'an yan sanda biyu da dan farar hula daya ne aka kashe a rikicin jihar Ondo

- A makon da ya gabata ne dai aka samu tashin hankali a jihar sakamakon zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS

- Kwamishinan yan sandan Ondo ne ya tabbatar da hakan a yayin gurfanar da wasu masu laifi

Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar jami’anta biyu da wani dan farar hula daya a rikicin da aka yi a makon da ya gabata a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS.

Kwamishinan yan sandan jihar, Bolaji Salami, wanda ya yi magana a yayin gurfanar da mutane 18 da ake zargi da sace-sace, ya ce an kashe jami’an yan sandan ne a garin Ore da Ondo.

KU KARANTA KUMA: Abun dariya abun haushi: An sace madubin idon gunkin Awolowo a Lagos

Yanzu Yanzu: An kashe jami’an yan sanda 2, da dan farar hula 1 a rikicin Ondo
Yanzu Yanzu: An kashe jami’an yan sanda 2, da dan farar hula 1 a rikicin Ondo Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Bolaji ya ce an far ma dan sandan na Ore ne da duka yayinda shi kuma na Ondo an kashe shi ne sannan aka cinna masa wuka a cikin mota, jaridar The Nation ta ruwaito.

ya kuma bayyana cewa dan farar hular da aka kashe ya kasance daya daga cikin tawagar mutum uku da suka yi yunkurin yin fashi a wani bankin zamani a garin Ondo.

A gefe guda, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Sun cigaba da satar dukiyoyin gwamnati wadanda suka hada da kayan tallafin COVID-19, kayan shaguna, kasuwanni da sauran dukiyoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng