Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello

Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello

- Gwamna Yahaya Bello ya zargi wasu yan Najeriya da karkatar da kudin COVID-19

- Gwamnan na jihar Kogi ya ce mutanen da suka karkatar da kudaden sun hada da jami’an gwanati da masu zaman kansu

- Bello ya soki irin rikon da aka yiwa rikicin korona a Najeriya

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi zargin cewa wasu yan tsiraru sun hamdame biliyoyin naira da ya kamata a yaki annobar COVID-19 da shi.

A cewar jaridar Daily Trust, Bello ya yi wannan zargi ne a wani hira da yayi da Channels TV.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa mutanen da suka hamdame kudaden sun hada yan Najeriya da ke gwamnati, wadanda basa cikin gwamnati, wasu da ke harkar kasuwanci da kuma yan tsiraru dake tsakani.

Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello
Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

Bello ya tuna cewa ya ja hankali game da yadda Najeriya ke tafiyar da annobar korona.

Ya jaddada cewar an hurewa yan Najeriya kunne tare da batar da su kan cutar.

Gwamnan ya ce sai da ya yi gargadin cewa akwai siyasa a cikin lamarin korona.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Yanzu haka bata gari sun bazama neman dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Kuje

A wani labari kuma, hawaye sun kubce wa Goddy Jeddy Agba, karamin ministan wutar lantarki, a ranar Talata, 27 ga watan OKtoba, yayin da yake zagayen duba asarorin da matasa suka tafka wa Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Agba ya fashe da kuka, bayan ganin irin aika-aikar da bata-gari suka yi a asibitin masu tabin hankali, inda suka lalata tsadaddun abubuwa.

Gwamna Ayade, ya bayyana irin dumbin dukiyar da jihar Cross River ke bukata don gyara duk abubuwan da aka bata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel