Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa

Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa

- Yan sanda a Jihar Adamawa sun cafke mutum 238 bisa zargin satar kaya a rumbunan ajiyar gwamnati da na jama’a

- An kuma yi nasarar kwato wasu kayayyaki daga hannun bata garin da suka sace su a yayin zanga-zangar EndSARS

- Rikici ya fara a jihar ne ranar Lahadi, bayan dandazon matasa sun mamaye dakunan ajiyan gwamnatin jihar a Yola, suka kwashe abincin tallafin korona da aka ba jihar

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama mutum 184 kan laifin sata a yayin zanga-zangar EndSars sannan ta kama wasu 54 da laifin take dokar kulle da aka saka a jihar.

Rundunar ta kuma yi nasarar kwato wasu kayayyaki da bata garin suka sata wadanda suka hada da taraktoci 35, adaidaita sahu 12, motoci tara, buhuhunan taki 742, buhuhunan masara 18, kujerun roba 95, inifam din kwastam takwas da sauransu.

Bata gari da suka fake da zanga-zangar EndSARS suna ta sace-sace a fadin kasar, sun daukaka hare-harensu a ranakun Lahadi da Litinin.

Sun yi ta afkawa rumbunan gwamnati da na daidaikun mutane suna ta kwasan duk abunda suka gani.

KU KARANTA KUMA: Sun ji uwar bari: Ɓata gari sun fara maido da kayan da suka sata a Adamawa

Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa
Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa Hoto: netstufs.com
Asali: UGC

An ci gaba da sace-sacen ko bayan da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya kaddamar da dokar kulle na sa’o’i 24 a ranar Lahadi, jariar The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar Adamawa, CP Olugbenga Adeyanju,wanda ya gabatar da masu laifin da kayayyakin da aka samo ga manema labarai a ranar Laraba, ya nuna rashin jin dadi da ganin cewa sace-sacen EndSARS ya gudana a Adamawa.

“Bamu taba samun korafe-korafe a kan SARS ba a jihar nan; matsalar da muke da ita kawai sune matasan Shila wanda muka magance,” in ji CP din, inda ya kara da cewar bai ga dalilin da yasa jihar ta fuskanci wannan mummunan al’amari ba a alilin EndSARS.

Ya kara da cewa, mutanen da suka yi satan da sunan zanga-zangar EndSARS sun kasance miyagu da ke amfani da damar rikicin EndSARS.

“Muna magana ne a kan bata gari ne; kawai shine magana saboda idan kuna neman tallafi ne kamar yadda masu zanga-zangar EndSARS ke yi, ba wai za ku je hukumar FRSC bane ko hukumar agaji ta Red Cross, ko UNICEF ko rumbunan mutane masu zaman kansu ba domin ba a ajiye tallafin korona a irin wadannan wurare,” in ji.

Ya ce ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun fara sintirin hadin gwiwa don tabbatar da aminci da dakile zauna-gari-banza daga kai wa dukiyoyin jama’a farmaki a jihar.

KU KARANTA KUMA: 2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

A wani labarin, Ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farooq ta bayyana cewa ma’aikatarta ta rabawa gwamnonin jihohi 36 kayan abinci har tan 70,000 a lokacin kullen annobar korona.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a zantawarta da sashin Hausa na BBC a ranar Talata a Zamfara, ministar ta ce ta kuma raba tirelolin shinkafa 145 zuwa wadannan jihohi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel