Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki

Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki

- Al'umman jihar Lagas sun shiga halin fargaba saboda rashin jami'an doka a titunan jihar

- Wannan al'amari ya ba bata gari damar cin karensu ba babbaka yayinda suka janye ragamar wasu manyan hanyoyi

- A yanzu dai mazauna jihar sun dukufa wajen rokon yan sandan da su dawo bakin aiki domin su kare rayukansu da dukiyoyinsu

Mazauna Lagas sun roki jami’an yan sanda da su koma bakin aiki sannan su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sun yi wannan roko ne a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, a kafofin soshiyal midiya sakamakon rashin yan sanda a titunan Lagas.

Mazauna Lagas sun tunatar da yan sandan cewa aikinsu shine kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda suka bukaci da su manta da mummunan al’amarin da ya faru a makon da ya gabata.

Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki
Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki Hoto: Businessamlive
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

Wasu mazauna yankin sun koka da ayyukan bata gari, wadanda suka mamaye manyan tituna da unguwanni tun bayan da yan sanda suka janye, yayinda wasu ke korafi a kan yadda masu tukin ababen hawa suka daina bin doka.

Musamman matukan motocin kasuwa, wadanda ke tsayawa da tuki ba bisa ka’ida ba.

Sulaimon Alamutu ya ce PWD, wata tashar tsayawar motoci a hanyar Agege, ta cunkushe gaba daya saboda rashin jami’an doka.

Wani dan jihar ya yi alhinin ko yaushe jami’an doka za su koma aiki.

A wata budaddiyar wasika zuwa ga yan sanda a Facebook, wata mata mai suna Safiya Musa, ta ba da hakuri a madadin yan Najeriya wadanda suka razana jami’an.

KU KARANTA KUMA: Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello

Ta rubuta: “Ya rundunar yan sandan Najeriya, dan Allah muna baku hakuri a madadin yan Najeriya wadanda suka razana ku. Sun yi wa kowa kudin goro, saboda haka muna masu baku hakuri.

“Yanzu mun san muhimmancinku, kuma mun gane cewa ba dukkaninku bane gurbatattu.

“Dan Allah ku daina fushi sannan ku taya mu kare rayuka da dukiyoyi, yayinda ku kuma sai ku cire bara gurbin cikinku. Mun san cewa da damanku kun yi sanyi a yanzu, amma dan Allah ku tuna Najeriya.”

A gefe guda, kwamishinan ƴan sandan Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata, ya ce sun kama mutum 520 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da ƙone-ƙone, fashi, kisan da kuma mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya lokacin zanga zangar Endsars.

Mr Odumosu ya shaidawa yan jarida a hedikwatar Ikeja, cewa an kama masu laifin ne a laifukan da aka aikata sakamakon karya doka lokacin zanga zangar EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel