Abdul Rahman Rashid
4128 articles published since 17 May 2019
4128 articles published since 17 May 2019
Yan ta'addan daular Islama a yankin Afrika ta yamma wato ISWAP sun kai mumunan hari garin Bambula a karamar hukumar Chibok inda sukayi awon gaba da kwamandan yan kato da gora wato JTF, Mohammed Abba.
Ministar walwala, jinkai da harkokin jin dadin al’umma, Sadiya Umar Faruq, ta bayyana dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi afuwa ga wasu daga cikin yan Boko Haram masu tayar da kayar baya.
Nakasassu a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da dokar hana sufuri da babur da Keke Napep a jihar Legas.
An dabawa wani ma'aikacin kamfanin raba wutan lantarkin AEDC wuka har lahira a ranar Talata a unguwar Kabusa, Abuja, yayinda aka ji wa abokin aikinsa mumunan rauni
Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun zabi Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani matsayin sabon kakakin majalisar a ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020.
Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Alhaji Aminu Shagali, ya yi murabus. An bayyana cewa Aminu Shagali ya yanke shawarar murabus ne ka shirye-shiryen da wasu yan majalisar ke yi na tsige shi.
Babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar Talata, ta kama tsohon kakakin jamiyyar Peoples Democratic Party PDP, Olisah Metuh, da kamfaninsa, Destra Investments Limited, da laifi daya cikin bakwai da hukumar EFCC take zarginsa
Yan Sanda sun kama wani matashi mai kimanin shekaru 26 mai suna Kamaldin Abu Sabo, wadda yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa a birnin Lafia dake Jihar Nasarawa.
Barandancin a jihar Neja ya dau sabon salo yayinda yan bindigan suka gargadi mutanen wasu garuruwan karamar hukumar Rafi su daina fita tsakanin karfe 4 na yamma zuwa 7 na safe saboda lokacin suka kai farmaki.
Abdul Rahman Rashid
Samu kari