Bara daban, Almajiranci daban - Shehin Malami Dakta Mansur Sokoto ya yabawa dokar hana bara

Bara daban, Almajiranci daban - Shehin Malami Dakta Mansur Sokoto ya yabawa dokar hana bara

Shahrarren masanin addinin Islama, Dakta Mansur Ibrahim Sokoto, ya yabawa gwamnatocin jihar Kano da Nasarawa kan haramta bara ga Almajirai.

Malamin ya bayyana cewa can dama babu wata alaka tsakanin bara da almajiranci. ya yi kira ga gwamnonin sun fito da wasu hanyoyin rage talauci da yunwa cikin masu aikin barace-barace.

A cewarsa: “Bara daban, almajirci daban. Matakin da jihohin Kano da Nasarawa suka dauka abin yabawa ne, da sharadin a fito da karfafan hanyoyin rage radadin talauci.“

Bara daban, Almajiranci daba - Shehin Malami Dakta Mansur Sokoto ya yabawa dokar hana bara
Shehin Malami Dakta Mansur Sokoto
Asali: Facebook

KU KARANTA Jami'ar jihar Kaduna ta sallami dalibai 80 kan laifin satar amsa

Gabanin Jawabin Dakta Mansur, kungiyar koli ta addinin Musullunci a jihar Kano, ta soki hukuncin gwamnatin jihar na haramta bara a kan titunan jihar da ta yi. Ta ce hakan bai dace ba kuma gwamnatin jihar ba ta dau lamarin ta yadda ya dace ba.

Ya jaddada cewa akwai bukatar a tantance wanne irin bara ce aka haramta kuma a saka duk masu ruwa da tsaki a harkar kafin a kaddamar da ita.

“Don haramcin yayi aiki, akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati da malaman tsangaya. Akwai bukatar tattaunawa, a gano kiyasin yawan yaran, dalilin hana bara da kuma sanin mutane nawa za a shigar. Akwai bukatar hada kai da wasu jihohi masu makwabtaka da jihar in har ana bukatar tabbatar lamarin,” yace.

Sheikh Khaleel ya yi kira ga gwamnatin da ta tuntubi duk masu ruwa da tsaki da kuma malamai don samar da mafita mai dorewa wajen kashe bara kwata-kwata.

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jihar.

Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin yara a Lafia a ranar Laraba.

Hakazalika gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata ya alanta dokar haramta bara ga almajirai a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel