Samun wuri: Yan bindiga sun sanya dokar ta baci a jihar Neja

Samun wuri: Yan bindiga sun sanya dokar ta baci a jihar Neja

Barandanci a jihar Neja ya dau sabon salo yayinda yan bindigan suka gargadi mutanen wasu garuruwan karamar hukumar Rafi su daina fita tsakanin karfe 4 na yamma zuwa 7 na safe saboda lokacin suke aiki.

Saboda haka, babu wani dan garin dake fitowa a lokutan kuma yan bindigan na cin karansu ba babbaka musamman satan shanu.

A cewar wani da garin, yan bindigan sun bayar da sanarwan ne bayan sun kashe mutane uku, wata mata da diyarta a yammacin ranar Asabar.

Bayan haka suka sace yan kauye 10.

KU KARANTA Zargin Almundahanan N1.35bn Shaidu sun kara bayyana gaban kotu kan Sule Lamido

Samun wuri: Yan bindiga sun sanya dokar ta baci a jihar Neja
Samun wuri: Yan bindiga sun sanya dokar ta baci a jihar Neja
Asali: Depositphotos

A farko, yan bindigan sun kai hari Anguwar Bulus da Tungan Makeri ranar Jumaa kuma suka kashe uwa da diyarta, yayinda suka jikkata wasu da yawa.

Na biyu, ranar Asabar sun yi garkuwa da yan kauye 10 a garin Maikujeri jima kadan bayan ziyarar da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya kai Kagara inda yaje ziyartar sansanin yan gudun hijra.

The Sun ta ruwaito cewa yan bindiga sun bukaci man fetur matsayin fansan wadanda suka sace a Tungan Makeri da Angwar Bulus.

“Na sani sarai an kaiwa yan bindigan man fetur na kimanin N80,000 cikin jarkoki cikin daji domin sakin wadanda suka sace.“

“Abubuwa daban-daban na faruwa a nanamma babu wanda ya damu. Wannan abin takaici ne.“ Yace

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng