Yanzu-yanzu: An kashe jami'in wutan lantarki yayinda yake kokarin yanke wuta a Abuja

Yanzu-yanzu: An kashe jami'in wutan lantarki yayinda yake kokarin yanke wuta a Abuja

An dabawa wani ma'aikacin kamfanin raba wutan lantarkin AEDC wuka har lahira a ranar Talata a unguwar Kabusa, Abuja, yayinda aka ji wa abokin aikinsa mumunan rauni

Ma'aikatan sun shiga unguwar Kabusa yanke wutan wadanda ake bi bashi kawai sai wani matashi ya kawo musu hari ta baya.

An kai gawarsa dakin ajiye gawawwakin Asibitin Garki dake Area 8, Abuja.

Shugaban hulda da jama'a na AEDC, Fadipe, ya tabbatar da rahoton.

Fadipe ya kara da cewa an garzaya da dayan ma'aikacin da ya jikkata asibiti kuma yana smaun sauki.

Yanzu-yanzu: An kashe jami'in wutan lantarki yayinda yake kokarin yanke wuta a Abuja
Yanzu-yanzu: An kashe jami'in wutan lantarki yayinda yake kokarin yanke wuta a Abuja
Asali: UGC

Fadipe ya ce hare-hare kan ma'aikatansu ya zama ruwan dare a birnin tarayya Abuja.

Ya bada labarin cewa wani jami'in hukumar Kwastam, Iliya Ayuba, ya kaiwa jami'insu hari a minna, hakazalika hare-hare daban-daban a Kabayi, Lokogoma, Gwagwalada da Jikwoyi, duka a birnin tarayya.

Fadipe yace kamfanin za ta dauki matakin da ya kamata a kai kuma ba zasu lamunci wannan cin mutunci ba.

Tuni an damke matashin da yayi kisan kuma yana tsare a ofishin yan sanda.

A bangare guda, Kamfanin watsa wutar lantarkin Nigeria ta sanar da yan Nigeria dasu shirya da karin kudin wutar lantarki na daga watan Afrilu domin samun walwalar wutar.

Darakta manaja na kamfanin watsa wutar lantarki TCN, Usman Mohammed, ya bayana hakan ranar Alhamis, yace gwamnati ta cigaba da sanya kudinta a bangaren wutar lantarki duk da bata bayyana hakan ba na tsawon shekaru shida da suka wuce.

Mohammed ya bayyana hakan ne yayin gyara wasu tsofaffin wayoyin watsa wutar lantarki da suka tsinke a karamar hukumar Alimosho-Ogba-Alausa-Ota dake birnin Ikeja.

Yace, “Muna aiki ne domin kamfanin watsa wutar lantarkinmu ta zama itace wadda tafi kowanne kamfani a duniya. Amma inaso in sanarwa yan Nigeria cewa hakan ba zai yiyu ba sai sun biya kudin wuta.

“Ina so in sanar da yan Nigeria cewa ba alaka tsakanin talauci da biyan kudin wutar lantarki.”

Ya kara da cewa Nigeria tafi kowace kasa saukin kudin wutar lantarki a nahiyar Afrika ta yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel