An kona Masallaci, an kashe 20, an jikkata 200 yayinda rikici ya barke tsakanin Musulmai da yan Hindu a Indiya

An kona Masallaci, an kashe 20, an jikkata 200 yayinda rikici ya barke tsakanin Musulmai da yan Hindu a Indiya

Akalla mutane 21 sun rasa rayukansu yayinda akalla 200 sun samu munanan raunika yayinda rikici ya barke tsakanin mabiya addinin Islama da mabiya addinin Hindu a kasar Indiya

Wannan rikici shine rikicin addini mafi muni cikin shekarun baya-baya a kasar Indiya.

A ranar Talata, matasan addinin Hindu sun bankawa Masallacin babbar birnin kasar Indiya, New Delhi, wuta.

Hakazalika sun kai hare-hare unguwannin Musulmai a rikicin kwana uku dake cigaba da gudana sakamakon dokar cin zarafin Musulmai da majaisar dokokin kasar ta samar.

Akalla mutane 200 sun jikkata kawo yanzu musamman Musulmai a birnin New Delhi yayinda yan sanda suka zuba ido ana kashe Musulmai, ana lalata dukiyoyinsu, ba tare da cewa uffin ba.

Ana zargin shugaban kasar Indiya, Narenda Modi, zuzuta makirci da kin jinin Musulmai a kasar.

Bayan kona Masallacin, matasan Hindu sun rataya tutar addininsu kan hatsumiyar Masallacin.

Kalli bidiyon Aljazeera kan rikicin

A bangare guda, Yan ta'addan daular Islama a yankin Afrika ta yamma wato ISWAP sun kai mumunan hari garin Bambula a karamar hukumar Chibok inda sukayi awon gaba da kwamandan yan kato da gora wato JTF, Mohammed Abba.

Wani mazauni ya bayyanawa TheCable cewa Yan ta'addan sun dira garin ne misalin karfe 4 na daren Laraba. Majiya ta bayyana cewa yan ta'addan sun dade suna zawarcin Mohammed Abba tun da yaki amsa bukatarsu.

An yi awon gaba da shi ne tare da wasu abokan aikinsa da ba'a gano ba har yanzu Yan kato da gora sun kasance masu taimakawa Sojoji wajen yakar yan tada kayar bayan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabashin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel