Budurwa ta caka wa saurayinta wuka har lahira akan N3,000

Budurwa ta caka wa saurayinta wuka har lahira akan N3,000

Yan sandan jihar Ogun sun damke wata budurwa, Idowu Abosede, da laifin dabawa saurayinta wuka, Aliyu Ibrahim, har lahira.

An damke wacce ake zargin, mai kimanin shekaru 18, ne a Sagamu bayan sun samu rashin jituwa tsakaninta da saurayinta akan N3,000.

A wani bayani daga kakakin yan sanda, Abimbola Oyeyemi, ranar Laraba, ya bayyana cewa budurwar tayi amfani da wuka wajen caka ma masoyinta a kirji.

Oyeyemi yace, “An kama wacce ake zargin bayan an samu kira daga Sarkin Hausawa a Sangamu cewa ita da saurayinta marigayi sun samu rashin jituqa ne akan N3,000 dalilin hakane yasa suka fara jan wuka a tsakaninsu sai yarinyar tayi nasarar chaka mai wuka a kirji har Lahira.”

“Bisa tambayoyin da aka ma budurwar, ta bayyana cewa ta kwana a wurin marigayin ne amma yayin data tashi tafiya da safe, sai ta dauki N3000 amma sai yace bazai bata duka ba, abinda ya haddasa fada kenan tsakaninsu.

“Ta kara da cewa Marigayin ne ya fito da wukar, a yayin da suke jayayya ne ya chaka wa kansa a kirji.”

Duk da haka, Mai magana da yawun yan sanda, ya bayyana cewa iyalan Marigayin sun bukaci da’a sakar musu gawar domin sitirtashi.

Budurwa ta caka wa saurayinta wuka har lahira akan N3,000
Budurwa ta caka wa saurayinta wuka har lahira akan N3,000
Asali: Facebook

KU KARANTA Bara daban, Almajiranci daban - Shehin Malami Dakta Mansur Sokoto ya yabawa dokar hana bara

A wani labari mai alaka, Yan Sanda sun kama wani matashi mai kimanin shekaru 26 mai suna Kamaldin Abu Sabo, wadda yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa a birnin Lafia dake Jihar Nasarawa.

Kwamandan yan sandar Jihar, Mahmud Gidado Fari, ya bayyanawa manema labarai cewa mahaifiyar sa ta kai kararsa wurin yan sanda cewa danta ya dade yana barazanar kasheta ba wani dalili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel