Dokar hana Babur: Nakasassu sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Legas

Dokar hana Babur: Nakasassu sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Legas

Nakasassu a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da dokar hana sufuri da babur da Keke Napep a jihar Legas.

Faifan bidiyo da hotuna da suka yadu a kafofin sadarwa ya nuna yadda nakassasun suka tare kofar shigan gidan gwamnatin jihar.

Za ku tuna cewa Gwamnatin jihar Legas ta haramta sana'ar tuka babur mai kafa biyu, watau 'Achaba', da babur mai kafa uku, da aka fi sani da 'adaidaita', a fadin kananan hukumominta guda shidda (LCDAs).

Kananan hukumomi 6 da sabuwar dokar da shafa sune kamar haka; karamar hukumar Apap da Apapa Iganmu, Lagos Mainland da Yaba LCDA a karamar hukumar Surelere, Itire-Ikate da Coker Aguda LCDAs, karamar hukumar Ikeja da Onigbongbo da Ojodu LCDAs.

Sauran sune; karamar hukumar Eti-Osa, Ikoyi-Obalende da Iru/Victoria Island LCDAs, karamar hukumar Lagos Island da Lagos Island ta gabas LCDA.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa dokar zata fara da karfinta daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2020.

Gwamnatin jihar ya bayyana cewa daukan wanna mataki yana daya daga cikin tsare-tsarenta na tsaftace hanyoyin cikin garin Legas da kuma kare jama'a daga illolin da wadannan hanyoyin sufuri (Achaba da adaidaita) ke haifar wa.

Kalli hotunan

Dokar hana Babur: Nakasassu sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Legas
Dokar hana Babur: Nakasassu sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Legas
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel