Yanzu-yanzu: Yan taaddan ISWAP sun kai hari Chibok, sun dauke kwamandan CJTF

Yanzu-yanzu: Yan taaddan ISWAP sun kai hari Chibok, sun dauke kwamandan CJTF

Yan ta'addan kungiyar daular Islama a yankin Afrika ta yamma wato ISWAP sun kai mumunan hari garin Bambula a karamar hukumar Chibok inda sukayi awon gaba da kwamandan yan kato da gora wato JTF, Mohammed Abba.

Wani mazauni ya bayyanawa TheCable cewa Yan ta'addan sun dira garin ne misalin karfe 4 na daren Laraba.

Majiya ta bayyana cewa yan ta'addan sun dade suna zawarcin Mohammed Abba tun da yaki amsa bukatarsu.

An yi awon gaba da shi ne tare da wasu abokan aikinsa da ba'a gano ba har yanzu

Yan kato da gora sun kasance masu taimakawa Sojoji wajen yakar yan tada kayar bayan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabashin Najeriya.

Mazaunin yace “Harbe-harben ya tashemu daga barcci, sai muka fara guduwa.“

“Yan taaddan sun shigo ne ta Ajigum Talala, wani sashen dajin da ISWAP ke da karfi. Sai suka garzaya wajen Abba kuma suka saceshi. Sun dade suna gargadinsa amma ya ki amincewa,“

“Sun yi garkuwa da mutanen da suka kasa gudu. Hakazalika sun kona dukiyoyi tare da motar alummar.“

KU KARANTA Oshiomole, manyan jiga-jigan APC da PDP sun dira kotun yayinda ake shirin sake duba shariar zaben gwamnan jihar

Yan tada kayar bayan sun kai wannan hari ne mako daya bayan harin da suka kai Korongilum a karamar hukumar Chibok inda suka kona muhallan jama

Wani mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa yan ta’addan sun shiga garin ne misalin karfe 6 na yamma kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Yace “Dawowar mutane gida daga gonakinke da wuya, sai yan taaddan suka shigo. Sun samu shiga ne ta Forfor, kuma mutane na guduwa yanzu.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel